Yadda Tinubu da Gwamnoni Suka Cimma Matsaya kan Kudirin Haraji

Yadda Tinubu da Gwamnoni Suka Cimma Matsaya kan Kudirin Haraji

  • Alamu sun nuna cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin Najeriya sun samu fahimtar juna kan ƙudirin haraji
  • Gwamnonin sun fitar da sanarwa, suka nuna goyon bayansu ga ƙudirin amma sun kawo sauye-sauyen da suke so yi kan harajin VAT
  • Majiyoyi sun bayyana yadda aka cimma yarjejeniya tsakanin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohin na Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Alamu suna nuna cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnoni sun samu daidaito kan ƙudirin haraji.

An samu ƙarin bayanai kan yadda shugaba Bola Tinubu da gwamnoni 36 na tarayyar Najeriya suka cimma matsaya kan batutuwan da suka shafi ƙudirin gyaran haraji.

Tinubu da gwamnoni
Tinubu da gwamnoni sun fahimci juna kan kudirin haraji Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Shugaba Tinubu ya yabi gwamnoni kan ƙudirin haraji

A jiya, shugaban ƙasa ya fitar da wata sanarwa yana yabawa gwamnonin, waɗanda ke magana a ƙarƙashin ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), bayan sun bayyana wasu sauye-sauye da suke so a yi ga ƙudirin.

Kara karanta wannan

Zargin neman cin hanci daga jami'o'i: Dan majalisa ya fadi yadda abubuwa suka kaya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar shugaban ƙasan na zuwa ne ƙasa da awa 24 bayan gwamnonin sun fitar da sanarwa inda suka bayyana matsayarsu kan ƙudirin haraji.

Shugaba Tinubu ya yabawa gwamnonin, yana mai cewa hakan ya nuna suna da niyya mai kyau kan ci gaban Najeriya.

Yadda Tinubu da gwamnoni suka cimma matsaya

Jaridar Daily Trust ta ce majiyoyi da suka san yadda Tinubu da gwamnonin suka cimma matsaya kan ƙudirin harajin, sun bayyana cewa an kammala cimma yarjejeniyar ne a Legas.

“An tabbatar da yarjejeniyar ne lokacin da gwamnonin suka kai ziyarar murnar sabuwar shekara ga Tinubu a gidansa da ke Legas."
"Shugaban ƙasa ya shaida musu cewa ya yi wannan shiri ne da kyakkyawar manufa, kuma yana son su ba shi dama domin ya tabbatar da hakan."

- Wata majiya

Wata majiya wacce ta tabbatar da hakan, ta ce duk da gwamnonin sun amince su goyi bayan ƙudirin gyaran haraji, sun nemi shugaban ƙasa ya yi musu rangwame kan wasu batutuwan da suka shafi ƙudirin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano, sun sace diyar babban attajirin dan kasuwa

Gwamnonin Arewa ba su nuna wata jayayya ba sosai, inda suka ce ya kamata su samu wani ƙwaƙƙwaran dalili da za su gaya mutanensu.

"Gwamnonin sun ce ra’ayin da ya mamaye yankin shi ne cewa dukkanin waɗannan ƙudirorin an kawo su ne domin su ƙara talauta yankin."

- Wata majiya

A ƙarshe dai, an cimma matsaya cewa gwamnonin za su koma Abuja don ganawa da kwamitin shugaban ƙasa kan gyaran haraji.

Bayan ganawar gwamnonin da shugaban kasa, sun jaddada aniyarsu ta yin aiki tare da gwamnatinsa wajen ci gaban ƙasa.

Gwamnatin Tinubu za ta ba ƙananan hukumomi kuɗaɗe

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta shirya fara ba ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun tarayya.

Hadimin shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa daga watan Janairun 2025, za a fara ba ƙananan hukumomin kuɗaɗensu kai tsaye.

Sunday Dare ya buƙaci jama'a da su karkatar da hankulansu kan yadda jihohi da ƙananan hukumomi suke kashe kuɗaɗensu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng