'Yan Hisbah Sun Yi Namijin Kokari a Kano, Sun Kwato Kudi Sama da Naira Biliyan 200

'Yan Hisbah Sun Yi Namijin Kokari a Kano, Sun Kwato Kudi Sama da Naira Biliyan 200

  • Rundunar Hisbah a jihar Kano ta ƙwato tare da maida kudade har Naira biliyan 212.3 ga masu su na halal a shekarar 2024
  • Mataimakin babban kwamandan Hisbah, Mujahideen Aminudden ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai kan nasarorin da suka samu
  • Ya ce rundunar ƴan sandan Musulunci ta kudiri aniyar cimma abubuwa da dama a sabuwar shekarar da aka shiga ta 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rundunar ƴan sandan Musulunci watau Hisbah ta jihar Kano ta sanar da cewa ta ƙwato Naira biliyan 212.3 tare da damƙa wa masu su na halal a shekarar 2024.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin mataimakin babban kwamandan Hisbah, Mujahideen Aminudden, yayin wata hira da manema labarai a Kano.

Sheikh Aminu Daurawa da yan Hisbah.
Hukumar Hisbah ya bayyana nasarorin da ta samu a 2024 da shirinta a 2025 Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Mujahideen Aminudeen ya yi karin bayani kan nasarorin da Hisbah ta samu a shekarar da ta gabata da shirinta na shekarar 2025, kamar yadda Leadership ta kawo.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hisbah ta kwato makudan kudi a 2024

Ya ce waɗannan makudan kudi da Hisbah ta ƙwato sun shafi rikice-rikice da suka danganci kasuwanci, gado, da kuma basussuka.

Mataimakin babban kwamandan ya ce bayan karɓo kudin, Hisbah ta bai wa masu su na halal ba tare da ɗaukar ko sisi ba.

Wannan nasara tana daya daga cikin ƙoƙarin Hisbah na tabbatar da adalci ga al’umma, musamman wajen warware matsalolin da suka shafi alakar zamantakewa da cinikayya.

“A 2024, mun karbi korafe-korafe guda 16,939 da suka hada da rikice-rikicen aure, kasuwanci, gado, rikicin al’umma, da matsalolin bashi.
"Mun samu nasarar warware rikice-rikice guda 7,884, wanda ya taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.”

- Mujahideen Aminudden.

Ayyukan da hukumar Hisbah ta yi a 2024

Ya kara da cewa Hisbah ta kai samame 885 a fadin jihar Kano, ta kama mutane 354 bisa laifuka daban-daban kuma an gurfanar da su gaban kotu.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan tankar mai ta sake fashewa a Najeriya, mutane 11 sun rasu

Haka nan, hukumar ta karbi kararraki 2,836 da suka danganci laifuffuka kamar bashin kudi, matsalolin haya, tsare-tsaren kasuwanci da rikice-rikicen gado.

"Abin da zai ba ku sha'awa shi ne duk wannan ayyuka da Hisbah ta yi kama daga kwato kuɗaɗe ba wanda ta ɗauki ko kwandala a matsayin lada, tana yi ne kyauta kuma dan Allah," in ji shi.

Abubuwan da Hisbah ta sa a gaba a 2025

Game da shekarar 2025, Mujahideen ya ce karkashin jagorancin kwamanda, Sheikh Aminu Daurawa, Hisbah ta kuduri niyyar cimma muradu guda biyar.

Ya faɗi muradun da suka hada da wayar da kan jama’a, rage talauci, gyaran tarbiyya, tallafa wa sana’o’i da bayar da jari, da kuma hada kai da duk wani mai bukatar zaman lafiya da ci gaban jihar.

Hukumar Hisbah ta jaddada aniyarta na ci gaba da tabbatar da adalci da zaman lafiya a Kano, tare da daukar matakai da za su rage rikici da kyautata rayuwar jama’a.

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Tinubu ya umarci sake fasalinta, matasa za su caɓa

Majalisa za ta karawa ƴan Hisbah albashi

Kun ji cewa Majalisar dokokin Kano ta yaba da ayyukan ƴan Hisbah ke yi a jihar, ta fara kokarin yadda za a kara masu albashi da alawus.

Hon. Albdulhamid Minjibir ya gabatar da kudiri a gaban majalisar dokokin Kano, wanda ya nemi a ƙara albashin ƴan Hisbah tare da duba yiwuwar maida su cikakun ma'aikata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262