Sanata Ta Fadi Abin da Arewa ke Tsoro a Kudirin Haraji, Ta Bukaci a bi Tsarin Sardauna

Sanata Ta Fadi Abin da Arewa ke Tsoro a Kudirin Haraji, Ta Bukaci a bi Tsarin Sardauna

  • Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta fede gaskiya kan ce-ce-ku-ce da ake yi a Arewa game da kudirin haraji
  • Sanata Natasha ta ce rashin shirin da Arewa ta yi ne ya haifar da damuwa kan kudirin da ake tattaunawa yanzu a majalisa
  • A bikin Tunawa da Sardauna a Kaduna, ta yi kira ga 'yan Arewa su rungumi hangen nesan Ahmadu Bello na bunkasa tattalin arzikin yankin
  • Ta nuna cewa Arewa na iya dawowa da martabar tattalin arziki idan shugabanni suka maida hankali kan ci gaba da farfado da masana'antu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kaduna - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana cewa damuwar Arewa kan kudirin haraji ya samo asali ne daga rashin shirin yankin.

Sanatar da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta ba yan yankin shawara yadda za su farfaɗo da tattalin arziki duba da manufar Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Sanata ta nemo mafita kan kudirin haraji a Arewa
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bukaci bin tsarin tattalin arziki na Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Natasha Akpoti-Uduaghan.
Asali: Twitter

Kudirin haraji: Sanata ta ba yan Arewa shawara

A wata sanarwa daga hadiminta kan harkokin watsa labarai, Israel Arogbonlo, Natasha ta bayyana hakan ne a lokacin bikin Tunawa da Sardauna a Kaduna, cewar jaridar BusinessDay.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Natasha ta bukaci ‘yan Arewa su rungumi hangen nesan Ahmadu Bello, wanda ya jagoranci bunkasar tattalin arzikin Arewacin Najeriya a shekarun 1950.

Sanatan ta yi nuni da cewa a shekarar 1959, Najeriya ta fitar da gyada zuwa Burtaniya da darajarta ta kai fam miliyan 27, kwatankwacin N3.6trn a yau.

A yanzu haka, idan za a fitar da gyada daga Najeriya zai tsaya kan $3trn kacal, The Nation ta ruwaito.

“Tun a shekarar 1959, Najeriya ta fitar da gyada zuwa Burtaniya da darajar fam miliyan 27, wanda yanzu ya kai N3.6trn.
“Har ma ragowar gyadar da aka fitar daga ciki ana kai wa Burtaniya a matsayin abincin dabbobi, amma yanzu, fitar da gyada daga Najeriya ya tsaya kan $3m.”

Kara karanta wannan

Su waye ke daukar nauyin ta'addanci? Hafsan tsaro ya fayyace gaskiya kan lamarin

“Masana'antar auduga ta Arewa ta mamaye kasuwar auduga ta Liverpool a London daga shekarun 1950 zuwa 1970, yayin da masana'antar Kaduna ta bunkasa da samar da dubban ayyukan yi."

- Natasha Akpoti-Uduaghan

Yadda masana'antun Arewa suka bunkasa yankin

Sanata Natasha ta kuma koka kan durkushewar masana'antar auduga ta Arewa, wacce ta mamaye kasuwannin Liverpool a Burtaniya kuma ta samar da ayyukan yi da yawa ta hanyar masana'antu.

Yanzu masana'antar auduga a Najeriya ba ta da wani ci gaba, amma wannan masana'antar a duniya tana samar da $21bn a shekara.

“Dalilin da ya sa Arewa ke jin tsoro kudirin haraji shi ne rashin shiri. Idan muna samun Naira tiriliyan 3.6 daga samfurin noma guda, za mu damu da gyare-gyaren?"
“Saboda haka, ya kamata mu tilasta wa shugabanninmu su rungumi tunanin ci gaba don farfado da masana’antu da kasuwanci, mu kasance daga matsayi na yalwar tattalin arziki ga yankinmu da kasa baki daya."

Kara karanta wannan

Bello Turji ya sake sauya mafaka, an gano shi da wasu rikakkun yan ta'adda 2, ya nadi bidiyo

- Natasha Akpoti-Uduaghan

An tattauna kan kudirin haraji a Majalisa

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta shirya gudanar da sauraron ra’ayi kan dokokin gyaran haraji, saboda gabatar da shi domin karatu na uku da amincewa.

Bayan tattaunawa mai zurfi da hukumomin gwamnati, an cimma matsaya kan batutuwan da suka shafi gyaran tsarin haraji a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.