"Ku Yi Haƙuri," Majalisa Ta Hargitse, Minista Ya Ga Takansa a Wurin Kare Kasafin Kudin 2025

"Ku Yi Haƙuri," Majalisa Ta Hargitse, Minista Ya Ga Takansa a Wurin Kare Kasafin Kudin 2025

  • 'Yan majalisa sun nuna bacin rai kan rashin gabatar da takardun kasafin kuɗin ma’aikatar albarkatun man fetur kafin zaman kare kasafin
  • Lamarin dai ya tayar da hayaniya a zaman kwamitin haɗin guiwa na majalisa ranar Alhamis har sai da minista ya ba da haƙuri
  • Bayan komai ya lafa, ƙaramin ministan albarkatun mai, Hon. Ekperikpe Ekpo ya yi wa ƴan Majalisar bayani kan kasafin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hayaniya ta barke a Majalisar Tarayya yayin zaman kare kasafin kuɗi na 2025 na ma’aikatar albarkatun man fetur ranar Alhamis da ta gabata.

Lamarin ya faru ne yayin gabatarwar ministan man fetur (Mai), Sanata Heineken Lokpobiri, tare da ƙaramin ministan albarkatun fetur (Gas), Hon. Ekperikpe Ekpo.

Zaman kare kasafin kudi.
Yan majalisa sun nuna ɓacin rai a lokacin kare kasafin ma'aikatar albarkatun man fetur Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Kasafin 2025: Majalisa ta nuna ɓacin ranta

Yan majalisar sun nuna bacin rai sosai saboda rashin gabatar da takardun kasafin kuɗin ma'aikatar a gabansu, kamar yadda Channels tv ta kawo.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani dan majalisa ya fusata ya gaza hakura har sai da ya tunkari ƙaramin ministan albarkatun man fetur kan laifin da suka yi.

Lokacin da abubuwa suka yi zafi, ministan albarkatun man fetur, Sanata Lokpobiri ya bayar da haƙuri kan rashin fahimtar da aka samu.

Ministan Tinubu ya ba Majalisa hakuri

Ya shaidawa kwamitin haɗin guiwar cewa ba da gangan aka yi jinkirin ba da takardun ba kawai dai wata yar tangarɗa da rashin fahimta aka samu.

Da yake kare kasafin, Ekpo ya yi bayanin cewa Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen magance matsalolin fashewar abubuwa a bangaren albarkatun man fetur.

Haka kuma, ƙaramin ministan ya bayyana ƙoƙarin gwamnatin wajen bunƙasa amfani da iskar gas mai tsabta watau CNG) a matsayin tushen makamashi.

Ekpo ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa wasu kamfanoni shida kudi Naira biliyan 222 domin samar da kayan more rayuwa na bangaren man fetur.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a Kudu kan kafa shari'ar Musulunci, an gano inda matsalar take

Bayan haka, ya ce gwamnati ta yi aiki tukuru domin yaɗa amfani da gas na CNG a ababen hawa a faɗin ƙasar nan.

Yadda ministan ya kare kasafin 2025

Kasafin kuɗin 2025 da aka ware wa ma’aikatar albarkatun man fetur ya kunshi haƙƙokin ma’aikata, gudanarwa, da manyan ayyukan ci gaba.

Bayan haka kuma ƴan majalisar sun taɓo batun kasafin kuɗin da aka ware wa ma’aikatar a shekarar 2024 da yadda aka aiwatar da shi da nasarorin da aka samu.

Majalisar ta yaba da gyare-gyare da aka samu a fannin mai da gas, ciki har da ƙoƙarin inganta amfani da matatun mai na zamani da kuma kara ƙarfin tace mai a cikin gida.

Majalisa ta koka da ƙasafin sabuwar ma'aikata

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar tarayya ta nuna matuƙar damuwa game da Naira biliyan 11.8 da aka ware wa sabuwar ma’aikatar raya dabbobi.

Ministan raya dabbobi , Idi Maiha tare da manyan jami'ai da shugabannin hukumomi sun yi bayani kan kudaden da ma'aikatar ke bukata da ƙalubalen da take fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel