"An Shigo da Yan Ta'adda daga Waje," Sojoji Sun Gano Masu Hannu a Sababbin Hare Hare

"An Shigo da Yan Ta'adda daga Waje," Sojoji Sun Gano Masu Hannu a Sababbin Hare Hare

  • Hedkwatar sojojin Najeriya (DHQ) ta ce wasu mayaka daga kasashen ketare sun shigo Najeriya domin karawa ƴan ta'adda karfi
  • Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba ya ce baƙin ƴan ta'addan na da hannu a munanan hare-haren aka kai kwanan nan
  • A ƴan makonnin nan, ƴan ta'adda sun kara zafafa kai hare-hare kan sansanin sojoji da fararen hula, inda aka rasa rayuka da dana

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babbar hedkwatar rundunar sojin Najeriya (DHQ) ta gano waɗanda ke da hannu a hare-haren da ƴan ta'adda suka kai kwanan nan a sassan ƙasar nan.

DHQ ta bayyana cewa ƙaruwar hare-haren da ake samu a Arewa maso Yamna da Arewa maso Gabas na da alaƙa da wasu ƴan ta'adda da suka shigo daga ƙasashen ƙetare.

Kara karanta wannan

Yadda dakarun sojoji suka hallaka 'yan ta'adda kusan 200 yayin artabu

Manjo Janar Edward Buba.
Sojojin Najeriya sun zargi wasu mayakan kasashen waje da taimakawa ƴan ta'addan ƙasar nan Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Facebook

Hedkwatar sojojin ta bayyana cewa ƴan ta'addan sun shigo Najeriya ne domin karfafa ƴan ta'addan cikin gida wajen kai sababbin hare-hare, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A 'yan makonnin da suka gabata, an sha fama da munanan hare-hare kan sansanonin sojoji da fararen hula, lamarin da ya kara dagula sha'anin tsaro a Najeriya.

Sojoji sun gano masu hannu a hare-hare

Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba ya ce rundunar soji ta alaƙanta waɗannan hare-hare da wasu mayaka da suka shigo daga yankin sahara.

Buba ya bayyana hakan ne a wurin taron manema labarai na farko a 2025 kuma na bankwana gare shi inda zai tashi daga matsayin kakakin hedkwatar sojojin Najeriya.

"Dawowar munanan hare-hare na da alaƙa da mayakan da suka shigi daga ketare da nufin ƙarafafa ƴan ta'addan cikin gida, waɗannan baƙin ƴan ta'adda sun shigo daga yankin Sahel.
"Ƙarin wani abu da ya taimaka wajen kai wannan hare-hare su ne masu bada haɗin kai daga cikin jama'a, wsɗanda ke aiki a matsayin ƴan leƙen asirin ƴan ta'adda, su ke kai bayanin motsin sojojji."

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya gargadi jama'a bayan 'yan ta'adda sun kashe manoma a Borno

- Manjo Janar Edward Buba.

Sojoji sun shirya tunkarar kowane kalubale

Sai dai dun wannan haɗin guiwa da ƙalubalen da ya tunkaro, rundunar sojin ta tabbatar da cewa dakarunta ba za su yi ƙasa a guiwa ba wajen kakkaɓe duk wani nau'in ta'addanci.

"Duk da haka sojojin sun san nauyin da ya rataya a wuyansu na kawo karahen ayyukan ta'addanci a ƙasar nan, duk da muna fuskantar koma baya amma ba za mu sare ba," in ji shi.

Buba ya ƙara da cewa rundunar sojin ta san cewa wannan yaƙin ba da dare ɗaya bane, amma duk rintsi dakaru za su ga bayan ƴan ta'adda kuma mutane za su zauna lafiya.

Yan ta'adda sun yi wa sojoji kwantan ɓauna

A wani labarin, kun ji cewa 'yan ta'adda da ake zaton mayaƙan Boko Haram ne sun kai wa sojoji da 'yan sa-kai hari yayin da suke ƙoƙarin kwaso gawarwakin manoma 40 da aka kashe a Borno.

Lamarin da ƙara ɗaga hankula musamman da wasu sojoji da dakarun CJTF suka ɓata ba a gansu ba bayan harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262