An Tarfa Ƴan Bindiga, Sun Gudo daga Jihohin Arewa Za Su Sake Faɗawa Tarko

An Tarfa Ƴan Bindiga, Sun Gudo daga Jihohin Arewa Za Su Sake Faɗawa Tarko

  • Gwamnatin jihar Oyo ta sha alwashin gano ‘yan bindigar da ke shigowa daga arewacin ƙasar, za a yi amfani da doka wajen hukunta su
  • Mai taimkawa Gwamna Seyi Makinde kan harkokin tsaro ya ce gwamnatin Oyo ta ɗauki matakan da miyagu ba za su samu wurin ɓuya ba
  • Ya ce Gwamna Makinde zai yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen rage cunkoso a gidajen gyaran hali

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo - Gwamnatin jihar Oyo karkashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta sha alwashin murƙushe duk ɗan bindigar da ya yi gigin shigowa jihar.

Gwamnatin Makinde ta bai wa al'ummar Oyo tabbacin cewa za ta ɗauki matakan da za su tsare rayuka da dukiyoyin kowa a lungu da saƙon jihar.

Gwamna Seyi Makinde.
Gwamnatin Oyo ta shirya muskushe dukkan ƴan bindigan da suka kwarara jihar Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

Jaridar Leadershirp ta tattaro cewa gwamnatin ta yi wannan furuci ne yayin da aka fara yada labarin cewa wasu ƴan bindiga daga jihohin Arewa sun fara shiga Oyo.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta ya ɗauki sabon salo, EFCC ta gayyaci mutum 7 su amsa tambayoyi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga za su faɗa tarkon gwamnatin Oyo

Hakan ya sa Gwamna Seyi Makinde ya kira kuma ya jagoranci taron majalisar tsaro domin duba wannan barazana da lalubo mafita don kare al'umma.

Da yake hira da manema labarai bayan taron, mai ba gwamna shawara kan tsaro, Fatai Owoseni ya ce tuni ka ɗana tarko tare da ɗaukar matakan zaƙulo miyagu da hukunta su bisa tanadin doka.

Fatai Owoseni, wanda tsohon kwamishinan ‘yan sanda ne, ya bukaci jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Oyo za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron rayukan al'ummarta, rahoton Punch.

Babu wurin ɓuya a jihar Oyo

Owoseni ya ce duba da kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro a cikin jihar, ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka ba za su sami wurin buya ba.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 sun ajiye siyasa gefe, sun ɗauki matakin kare jihohinsu daga ƴan ta'adda

Ya kuma bayyana cewa jihar Oyo tana aiki tare da makwabtan jihohi don tabbatar da tsaron iyakokinta da hana shiga ta haramtacciyar hanya.

Haka nan kuma ya ce Majalisar tsaron za ta gudanar da manyan taruka da za su haɗa shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya.

Gwamnatin Oyo za ta jawo kowa a jiki

"Shugabannin ƙananan hukumomi suna da kusanci da jama’a, haka kuma sarakunan gargajiya suna kusa da mutanen yankunansu, sun san su sosai.
"Idan muka haɗa kansu wuri guda a tsarin tsaro, za mu yi kokarin jawo kowa. Tsaro hakki ne na kowa, kuma kowa na da rawar da zai taka wajen tabbatar da cewa jiharmu ta tsira daga ‘yan bindiga,” in ji shi.

Ya kara da cewa majalisar ta tattauna batun rage cunkoson gidajen gyaran hali, yana mai cewa jihar za ta yi amfani da ikon yin afuwa domin sakin wasu daga cikin fursunoni.

"Haka kuma, majalisar ta tattauna batun kula da lafiya da walwalar fursunoni kuma an bayar da shawarar a saka su a cikin tsarin Inshorar Lafiya na jihar Oyo."

Kara karanta wannan

Zargin siyasantar da masarauta: Gwamna ya sha alwashin kare ta, zai hukunta masu laifi

Makinde ya nuna damuwa da lamurran tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya koka kan barazanar tsaro da ke tunkaro jihar Oyo a Kudu maso Yammacin Najeriya.

Gwamna Seyi Makinde ya ce ya samu labarin wasu 'yan ta'adda sun kafa sansani a kusa da inda ya yi bikin murnar karin shekara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262