"Ya Cancanta," Gwamna Abba Ya Ciri Tuta, NLC Ta ba Shi Lambar Yabo a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu lambar yabo ta 'gwamna mai kishin ma'aikata' daga kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) reshen Kano
- Ma'aikatan gwamnatin Kano sun yi farin ciki da wannan lambar yabo, sun ce kungiyar NLC ta ba wanda ya cancanci a karrama shi
- Gwamnatin Abba ta dauki matakai kamar biyan basussukan fansho, tabbatar da biyan albashi a lokaci da horar da ma’aikata don kara musu kwarewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Kungiyar kwadago (N#C) reshen jihar Kano ta ba Gwamna Abba Kabir Yusuf lambar yabon, '"Gwamnan da ya fi nuna kishin ma'aikaikata,"
Tuni gwamnan ya fara shan ruwan yabo daga ma'aikatan gwamnatin Kano, waɗanda suka bayyana wannan lambar yabo da cewa ta dace da wanda aka ba.
Tribune Nigeria ta rahoto cewa lambar yabon ta kasance wata shaida mai karfi da ke nuna irin jajircewar gwamnan wajen inganta walwalar ma’aikatan gwamnati a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa NLC ta ba Gwamna Abba lambar yabo?
NLC ta zaɓi bai wa Abba Kabir wannan lambar yabo ne saboda irin tsare-tsaren da gwamnatinsa ta aiwatar da suka shafi inganta rayuwar ma’aikata da kare mutuncin su.
Gwamnatin Kano ta aiwatar da tsare-tsare da ke tabbatar da tsare ayyukan ma’aikata, biyan albashi a kan lokaci, da kuma tabbatar da cewa yanayin aiki ya dace da bukatu.
Martanin ma'aikatan gwamnatin jihar Kano
A cewar shugaban ma’aikatan jihar Kano, Abdullahi Musa, gwamnan ya nuna cewa jin dadin ma’aikata na daga cikin manyan abubuwan da ya fi bai wa muhimmanci.
Ya bayyana cewa gwamnatin Abba ta dauki matakai masu muhimmanci wajen biyan basussukan fansho da suka dade ba a biya ba.
Wannan mataki ya taimaka wajen rage damuwa da matsalolin da ma'aikatan da suka yi ritaya ke fuskanta a halin matsin rayuwar da ake ciki.
Wasu daga cikin ayyukan gwamnan Kano
Bugu da ƙari, gwamnatin Abba Gida-Gida ta tabbatar da biyan albashi da fansho a kan lokaci, wanda hakan ya karawa ma’aikata kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wurin aiki.
Haka kuma, ta mayar da hankali kan horar da ma’aikata da kuma samar da gyare-gyaren da za su kara musu kwarewa a fannoni daban-daban.
Wannan lambar yabo ta NLC ta jaddada cewa manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf sun kasance wani ginshiƙi na ci gaba mai dorewa a jihar Kano.
Tsare-tsaren gwamnan sun ba ma’aikata damar jin dadin ayyukansu, wanda hakan ke haifar da karin kwazo da kuma ingantaccen shugabanci.
A cewar ma'aikatan Kano, lambar yabon ta ƙara jaddada cewa Gwamna Abba ya kere tsara wajen inganta jin daɗinsu, wanda ke da muhimmanci wajen kawo ci gaba ga al'umma.
Gwamnan Kano ya kwato motoci 12
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya ware motocin da za su sauƙaƙa wa ɗaiban manyan makarantu a fannin sufuri.
Gwamnan ya ƙwato motocin ne daga gwamnatin da ta gabata, inda aka gyara su sannan aka miƙawa ma'aikatar ilimi mai zurfi domin jigilar ɗalibai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng