'Yan Ta'adda Sun Farmaki Sojoji a Borno, Jami'ai da Dama Sun Bace

'Yan Ta'adda Sun Farmaki Sojoji a Borno, Jami'ai da Dama Sun Bace

  • Ƴan ta'adda sun sake yin ta'asa bayan kisan manoma 40 a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Sojoji da fararen hular da suka je ɗauko garwarwakin ƴan ta'ddan sun fuskanci harin kwanton ɓauna daga wajen ƴan ta'addan
  • Majiyoyi sun bayyana cewa da yawa daga cikin sojoji da fararen hular ba a san inda suke ba bayan farmakin da ƴan ta'addan suka kai musu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Ƴan ta'adda sun kai wa sojoji da fararen hula farmaki yayin da suke kan aikin ɗauko gawarwakin manoma 40 da suka kashe a Borno.

Ƴan ta'addan dai sun kashe manoman ne a ranar Asabar a ƙauyen Dumba, da ke Baga, cikin ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

'Yan ta'adda sun farmaki sojoji a Borno
'Yan ta'adda sun yi wa sojoji kwanton bauna a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce majiyoyin tsaro da suka nemi a sakaya sunansu sun bayyana cewa mayakan ISWAP ne suka kitsa farmakin na ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamna ya daina ɓoye ɓoye, ya fadi manufar sojojin da suka kashe bayin Allah a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An nemi jami'an tsaro an rasa a Borno

Majiyoyin sun ce sojojin da ba a san adadinsu ba, da fararen hula 54 da suka haɗa da mafarauta, jami'an tsaro na ƴan sa-kai, da ƴan CJTF ne ba a san inda suke ba.

Wani mamba na CJTF ya ce mutum ɗaya ne kawai daga cikin mutum 54 da aka tura aikin ya dawo Baga, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Ya ce sojojin sun yi ƙoƙarin daƙile harin, amma ƴan ta'addan sun rinjaye su saboda yawan makaman da suke da su.

Game da ko akwai waɗanda suka rasa rayukansu, sai ya kada baki ya ce:

"Har yanzu ba a iya tantance hakan ba saboda babu wanda ya san abin da ya faru. Mutumin da ya dawo shi kaɗai ba shi da cikakkiyar natsuwar da zai bayyana abin da ya faru."

Sai dai wata majiya ta tsaro ta ce wasu daga cikin sojojin da aka ƙara turawa sun tsere inda suka koma sansaninsu.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun ci gaba da ta'addanci a Borno, sun yi barna mai yawa

Ƴan ta'adda sun yi wa sojoji kwanton ɓauna

Majiyar ta ce ƴan ta'addan sun kai wa sojojin hari ne a tsakiyar hanyar zuwa Dumba bayan sun gano gawarwakin wasu manoma sun binne su.

“Sun ga gawarwakin manoma da aka kashe a kan hanyarsu ta zuwa Dumba, sun birne gawarwaki 15, amma daga baya ƴan ta'addan sun farmake su yayin da suke shirin ci gaba da tafiya zuwa Dumba."
“Da yawa daga cikin sojoji da fararen hula da suka fara tafiya a rukunin farko sun ɓace tun ranar Talata. Ba mu san ko suna shawagi a daji ne ko kuma ƴan ta'adda ne suka kama su."

- Wata majiya

Wani 'dan CJTF ya ce lamarin akwai baƙin ciki da takaici, inda ya yi addu'ar Allah ya bayyana su.

"Yanayin abin tsoro ne kuma abin bakin ciki. Ba zan iya ba da adadin waɗanda har yanzu ba su dawo ba, amma muna addu’ar su dawo lafiya."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi wa 'yan bindiga kofar rago, an tura tsageru barzahu

- Wani mamban CJTF

Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makamai sun kai hsri a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas.

Ƴan ta'addan waɗanda suka kai harin a ƙaramar hukumar Chibok, sun ƙona gidaje masu yawa tare da wata coci da mabiya addinin Kirista suke amfani da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng