Ana Shirin Kara Farashin Fetur a Najeriya, NNPCL Ya Tara wa Gwamnati Naira Tiriliyan 10
- Kamfanin mai na ƙasa, NNPCL ya ce ya tara Naira tiriliyan 10 kuma ya tura su asusun gwamnatin tarayya daga Janairu zuwa Satumba, 2024
- Shugaban NNPCL, Malam Mele Kyari ne ya bayyana hakan a lokacin da ykae kare kasafin kamfanin na shekarar 2025 a gaban Majalisar tarayya
- Mele Kyari ya nemi a gudanar da binciken kwakwaf kan kudin da aka kashe wajen daidaita farashin fetur daga Janairu zuwa Satumba 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kamfanin mai na Najeriya (NNPCL), a ranar Laraba, ya bayyana cewa ya tura Naira tiriliyan 10 zuwa asusun tarayya daga farko zuwa watan Satumba a shekarar 2024.
Shugaban kamfanin, Mele Kyari, ya ce sun kuma fitar da Naira tiriliyan 3.5 a matsayin ribar kamfani bayan haraji da kudi shiga na bara.
Kyari ya bayyana hakan ne yayin kare kasafin kudin NNPCL na 2025 a gaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar dattawa da ta wakilai a Abuja, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ne na ɗaya wajen biyan haraji
Ya ce NNPCL shi ne kamfani ɗaya tilo a Najeriya da ke wallafa cikakken bayanin asusun kuɗinsa, abin da ya shiga da abin da ya fita a duk shekara.
Haka kuma, ya ce NNPCL shi ne na farko wajen mai biyan haraji da kuma samun riba ga masu zuba hannun jari a ƙasar nan.
Malam Mele Kyari ya yi kira da a gudanar da binciken kwakwaf kan kudaden da aka kashe wajen daidaita farashin man fetur daga Janairu zuwa Satumba 2024.
Kamfanin mai ya nemi a yi binciken kudi
Ya ce kafin ranar 1 ga Oktoba 2024, NNPCL, kamar yadda dokar PIA ta shimfida, shi ke da alhakin tabbatar da wadatar man fetur a ƙasar, kuma hakan na buƙatar tantance kuɗin da kamfani ya samu da wanda ya biyo bashi.
"Tsarin lissafin kudi na kamfanin NNPCL a fili yake kuma ana wallafa shi a duk shekara, hakan ya sa ya zama kamfani ɗaya tal da baya ƙunbiya-kunbiya."
"Kuma shi ne kamfanin da ya fi biyan haraji da samun kazamar riba ga masu zuba hannun jari a fannin kasuwancin mai," in ji Kyari.
Shugaban kamfanin ya kuma sanar da cewa hasashen kudaden shiga na 2025 zai fito bayan taron kwamitin gudanarwa na NNPCL wanda za ayi nan da makonni biyu.
Mele Kyari ya ce kasafin kudin na shekarar 2025 abu ne da zai yiwu kuma za a iya cimma nasara cikin sauƙi.
Yadda NNPCL ke tarawa gwamnati kudin shiga
Kyari ya bayyana cewa ba lallai ba ne kamfanin ya ci gaba da tura kuɗi zuwa ssusun hadaka kai tsaye ba, duba da sabbin dokokin da ke jagorantar ayyukan NNPCL.
A cewarsa, kamfanin a yanzu yana aiki ne a wani tsari na daban, inda gudunmawar da yake bayarwa take zuwa ne daga riba da kuma haraji maimakon turawa kai tsaye.
Farashin man fetur zai iya tashi a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa ƙungiyar dillalan mai IPMAN ta ce farashin litar fetur zai iya haura N1,000 saboda karin harajin da hukumar NMDPRA ta yi a kwanan nan.
Shugaban IPMAN ya bayyana cewa ko da sun yi ƙarin ya kamata ƴan Najeriya su sani cewa ba daga matatar Ɗangote ba ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng