Tsohon Sanata, Shehu Sani Ya Fadi Silar Lalacewar Lamura a Najeriya

Tsohon Sanata, Shehu Sani Ya Fadi Silar Lalacewar Lamura a Najeriya

  • Tsohon Sanata Shehu Sani ya bayyana takaicinsa na kisan Sir Ahmadu Bello da sauran manyan 'yan siyasa a juyin mulkin 1966
  • Sanata Shehu Sani, wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya ya ce kisan ya zama tushen fitina da har yanzu ke addabar Najeriya
  • 'Dan siyasar ya ce Ahmadu Bello ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa jama’arsa da kasarsa ba tare da tara abin duniya ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa har yanzu Najeriya tana fama da illar kisan Sir Ahmadu Bello, tsohon Firimiyan Arewa.

Sir Ahmadu Bello, wanda aka fi sani da Gamji, ya kasance babban dan siyasar Arewacin Najeriya, ya zama Firimiya na farko kuma na karshe daga 1954 har zuwa mutuwarsa.

Kara karanta wannan

"Allah ya albarkaci Najeriya," Hamza Al Mustapha ya taɓo batun kisan Sardauna

Shehu
Sanata Shehu Sani ya yi takaicin juyin mulkin 1966 Hoto: @ShehuSani
Asali: Twitter

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Shehu Sani ya bayyana cewa Sardauna, tare da sauran manyan 'yan siyasa sun mutu a juyin mulkin 1966 da ya kashe mutane da ya bar kasar a wahala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Thisday ta ambato sunayen manyan sojojin da suka jagoranci wannan juyin mulki sun hada da Manjo Emmanuel Arinze Ifeajuna da Manjo Chukwuemeka Kaduna Nzeogwu.

Sauran su ne Manjo Chris Anuforo, Manjor Tim Onwutuegwu, Manjor Chudi-Sokei, Manjo Adewale Ademoyega, Manjo Don Okaforanjo John Obieno da karin wasu mutum hudu

Sanata Shehu Sani ya yi takaicin kisan Sardauna

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Shehu Sani ya bayyana cewa kisan Sardauna da sauran manyan ‘yan siyasa a shekarar 1966 ya zama 'tushen fitina' da har yanzu ke addabar Najeriya.

Ya ce Sardauna ya yi duk abin da ya kamata don jama’arsa da kasar baki daya, kuma ya koma ga Allah ba tare da ya tarawa kansa dukiya ko ya mallaki kadara a jihar Kaduna da ya zauna ba.

Kara karanta wannan

Sarki 1 ne a Kano: Fitaccen lauya a Najeriya ya yi bayanin hukuncin kotu

Sanata Sani ya ce;

“Ga mu da ke Kaduna inda tsohon Firimiyan Arewa ya rayu, ya jagoranta kuma aka kashe shi cikin zalunci, ba mu taba samun wani gida, mota ko kamfani da aka alakanta da sunansa ko na ‘yan uwansa ba.

Shehu Sani ya fadi illar kisan Sardauna

Tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani ya bayyana cewa kisan Sardaunan Sakkwato da sauran manyan ‘yan siyasa a Najeriya shi ne silar kalubalen da suka addabi kasar nan.

Ya wallafa cewa;

“Bayan an kashe shi, an kwashe dukiyarsa zuwa gidan iyalinsa a Sakkwato. Marigayi Sardauna ya yi komai ga jama’arsa da kasarsa."
“Kisan shi da na sauran manyan mutanen kasar a shekarar 1966 ya zama tushen fitina da har yanzu Najeriya ke fama da ita. Allah ya ji kansu da duk wadanda suka mutu a wannan juyin mulki. Ameen.”

Sanata Sani ya nemi a karrama sarakunan Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Shehu Sani ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da a karrama jaruman da suka sadaukar da rayukansu wajen kare al'umma daga mulkin mallaka.

Kara karanta wannan

Sanatan Arewa ya faɗawa gwamnatin Tinubu dabarar murƙushe ƴan ta'adda cikin sauƙi

A wata ziyara da ya kai makabartar wasu sarakunan Arewa a Lokoja, Sanata Sani ya nuna muhimmancin tunawa da sadaukarwar da suka yi wajen yaki da turawan mulkin mallaka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.