"Allah Ya Albarkaci Najeriya," Hamza Al Mustapha Ya Taɓo Batun Kisan Sardauna

"Allah Ya Albarkaci Najeriya," Hamza Al Mustapha Ya Taɓo Batun Kisan Sardauna

  • Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai albarka, amma rashin tsari ya hana ƙasar amfani da damarmakin da Allah ya bata
  • Ya ce dagewar marigayi Sardaunan Sakkwato kan tace man fetur a cikin gida da kuma neman ‘yancin tattalin arzikin na cikin dalilan kashe shi
  • Al-Mustapha da Malam Balarabe Rufai sun yi kira ga jagororin Arewa da su yi koyi da Sardauna wajen bunkasa ilimi, tattalin arziki, da mutunta sarakuna don farfaɗo da yankin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Manjo Hamza Al-Mustapha ya jaddada muhimmancin tashi tsaye da kuma ɗaukar matakan gaggawa wajen magance matsalolin da suka addabi Najeriya.

Tsohon dogarin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Marigayi Sani Abacha ya ce Allah ya yi wa Najeriya albarka da ni'ima amma ƙasar ba ta da tsari mai kyau.

Kara karanta wannan

Tinubu ya jaddada shirin ragargazar 'yan ta'adda a fadin Najeriya

Manjo Hamza Al-Mustapha.
Hamza Al-Mustapha ya ce Najeriya ba ta da tsari amma Allah ya mata albarka da yawa Hoto: Dr. Hamza Al-Mustapha
Asali: Facebook

Al-Mustapha ya bayyana hakan ne a bikin tunawa da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato a Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Al-Mustapha ya jaddada muhimmancin ɗaukar mataki cikin gaggawa kan matsalolin da ke damun ƙasa tun kafin abin ya gagara.

Hamza Al-Mustapha ya tuna rayuwar Sardauna

Da yake tunanwa da hangen nesan Sardaunan Sakkwato, Al-Mustapha ya ce rashin tsari ne ya hana Najeriya cin gajiyar damarmakin da take da su.

Ya kuma tuna rikicin shekarar 1963 kan albarkatun mai, yana mai bayyana cewa dagewar Sardauna kan cewa dole a tace mai a cikin Najeriya na daga cikin dalilan da suka sa aka kashe shi.

Wasu dalilan da suka sa aka kashe Sardauna

"Kafewar da marigayi Sardauna ya yi kan dole a rika tace ɗanyen mai a cikin gida Najeriya na daga cikin muhimman dalilan da suka sa aka kashe shi.
"Sardauna ya yi ƙoƙari sosai don tabbatar da cewa tattalin arzikin Najeriya ya dogara da kansa, amma wannan hangen nesa bai cika ba.”

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Dalilin da ya sa Gwamna Bala ke sukar tsare tsaren Bola Tinubu

- Hamza Al-Mustapha.

Al-Mustapha ya damu da rashin ci gaban Arewa

Al-Mustapha ya nuna damuwarsa kan yadda yankin Arewa ya zama koma baya tun bayan rasa jagorori irinsu Sardauna masu hikima da hangen nesa.

"Don dawo da martabar Arewa, tsaro, ilimi da tattalin arziki, dole ne mu mutunta sarakunan gargajiya tare da farfaɗo da dabi’un Sardauna kamar jarumta, gaskiya, haɗin kai, da hangen nesa.”

Dabarun da ya kamata Arewa ta yi

Tun farko a wurin taron, shugaban ƙungiyar sake gina Arewa ta RAID, Malam Balarabe Rufai, ya yi kira ga shugabannin Arewa da su yi koyi da hangen nesa da dabarun jagorancin marigayi Sir Ahmadu Bello.

Ya bayyana cewa Sardauna ya mayar da hankali kan ilimi, ci gaban noma, da inganta ababen more rayuwa.

Dalilin ganawar Al-Mustapha da El-Rufai

A wani labarin, mun kawo maku cewa Majo Hamza Al-Mustapha ya yi bayanin dalilin ganawarsa da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.

Al-Mustapha, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce ganawar tare da jagororin jam'iyyar SDP na da alaƙa da halin da ƴan Najeriya ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262