"Ina da Mafita amma ba Zan Taimaka ba," Sarki Sanusi Ya Yi wa Shugaba Tinubu Tatas

"Ina da Mafita amma ba Zan Taimaka ba," Sarki Sanusi Ya Yi wa Shugaba Tinubu Tatas

  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce ba zai taimakawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gyara kura-kuran da ta yi a tsare-tsarenta ba
  • Sarkin Kano na 16 ya bayyana cewa duk da yana da abokai a gwamnatin amma ba su ɗauke shi a matsayin aboki ba saboda yadda suke mu'amalantarsa
  • Duk da an maido da shi sarauta, gwamnatin tarayya ta ci gaba da goyon bayan magabacinsa, Aminu Ado Bayero

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa ba zai taimaka wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen gyara manufofin da ke illata al'umma ba.

Sarki Sanusi ya yi wannan furuci ne a ranar Laraba a Lagos, lokacin da ya jagoranci taron cika shekaru 21 na Fawehinmiism watau lakcar shekara-shekara da aka saba shiryawa ta Gani Fawehinmi, 2025.

Kara karanta wannan

Sarki 1 ne a Kano: Fitaccen lauya a Najeriya ya yi bayanin hukuncin kotu

Muhammadu Sanusi II.
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya ce ba zai gyarawa gwamnatin Tinubu kuskuren da ta yi ba Hoto: @MasarautarKano
Asali: Twitter

Ya ce akwai abubuwan da zai yi bayanin kuskuren da aka yi da yadda za a gyara don kaucewa shiga wani hali amma ya zaɓi ya tsame hannunsa, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Sarki Sanusi ba zai taimaka ba?

Basaraken ya bayyana cewa ya zaɓi ya kama bakinsa ba tare da taimakawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba saboda yadda take mu'amalantarsa bai masa daɗi ba.

"Ina da abubuwan da zan faɗa da suka saɓawa tsarinsu, waɗanda suka yi bayanin halin da muke ciki da yadda aka hango shi tun farko, galibi za a iya magance su amma ba zan faɗa ba."
"Na zaɓi na kama baki na daina yin magana kan tattalin arziki ko gyare-gyare domin idan na bude baki na yi magana, hakan zai amfanar da wannan gwamnati, ni kuma ba na son taimaka masu."

- Sarki Muhammadu Sanusi II.

Babu nagartattun mutane a gwamnatin Tinubu

Sanusi II ya ƙara cewa duk da yake yana da abokai a cikin gwamnatin Tinubu amma yadda ba sa nuna halin abokantaka ya sa shi ma ya kama kansa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya jaddada shirin ragargazar 'yan ta'adda a fadin Najeriya

A ruwayar Channels tv, Sarkin ya ƙara da cewa:

"Ba su da mutane nagartattu da za su gaya masu gaskiya ko su yi wa mutane bayani, ni dai ba zan taimaka ba, da farko na fara haska masu amma yanzu na tsame hannu na."
"Su ya rataya a kansu su fito su yi wa ƴan Najeriya bayanin dalilin da yasa suka aiwatar da manufofinsu."

Sarki Sanusi ya hango halin da za a shiga

Duk da haka, ya ce halin da ake ciki a yau ba sabon abu ba ne, domin an riga an yi hasashen faruwar hakan shekaru da dama da suka gabata.

“An gargadi mutane shekarun da suka shige cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, za a kawo wannan matakin, amma suka rufe idonsu suka ƙi yin abin da ya kamata," in ji sarki.

Sanusi, wanda aka tsige daga sarautar Sarkin Kano a 2020 lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya koma kan sarauta a 2024 bayan NNPP ta karɓi mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bugi karji kan darajar Afrika a Qatar, ya fadi sirrin cigaban nahiyar

Har yanzu sarautarsa tana fuskantar ƙalubale daga gwamnati mai mulki a tarayya, wacce har yanzu ta na goyon bayan magabacinsa, Aminu Ado Bayero.

Sanusi II ya yi magana kan hukuncin kotu

Kuna da labarin cewa Sarki Muhammadu Sanusi ya buƙaci Kanawa su dage addu'ar samun zaman lafiya da kariya da fitintinu.

Sanuso II ya yi wannan magana ne yayin da yake martani kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke game da rikicin sarautar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262