Watanni bayan Tausaya Wa Yan Najeriya kan Halin Kunci, Yar Majalisar Tarayya Ta Rasu

Watanni bayan Tausaya Wa Yan Najeriya kan Halin Kunci, Yar Majalisar Tarayya Ta Rasu

  • An shiga jimami bayan sanar da rasuwar yar majalisar wakilai, Hon. Adewunmi Onanuga a yau Laraba 15 ga watan Janairun 2025
  • An tabbatar da rasuwar marigayar a yau bayan fama da rashin lafiya kamar yadda mai magana da yawun Majalisar ya sanar dazu
  • Onanuga, da aka fi sani da "Ijaya", ta yi fice a matsayin 'yar siyasa mai hazaka kuma mai kishin ci gaban al'umma da mata domin inganta rayuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An tabbatar da rasuwar mataimakiyar mai tsawatarwa a Majalisar Wakilan tarayya, Hon. Adewinmi Onanuga.

Marigayiyar ta rasu ne tana da shekaru 59 a yau Laraba 15 ga watan Janairun 2025 bayan ta sha fama da jinya na wani lokaci.

Yar Majalisar Wakilai a Najeriya ta rasu
An rashi a Majalisar Wakilai yayin da Hon. Adewunmi Onanuga ta yi bankwana da duniya. Hoto: @HouseNGR.
Asali: Twitter

An sake rashin 'yar Majalisar Wakilai a Najeriya

Kara karanta wannan

Gwamnoni, shugaban majalisa sun shiga jerin mutane 565 da Wike ya kwace filayensu a Abuja

Mai magana da yawun Majalisar, Akin Rotimi, shi ya sanar da rasuwar Onanuga cikin wata sanarwa da shafin Majalisar ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rotimi ya ce Onanuga, wadda ke wakiltar mazabar Ikenne/Sagamu/Remo ta Arewa a jihar Ogun, ta rasu a ranar Laraba bayan fama rashin lafiya.

"Cikin alhini da bakin ciki majalisar wakilai ke sanar da rasuwar Rt. Hon. Adewunmi Oriyomi Onanuga."
"An fi saninta da suna ‘Ijaya', Onanuga ta zama abin yabo saboda hazakarta, kishinta, tawali’u, da kuma jajircewarta kan inganta al’umma."
"Gagarumar gudunmawarta ga siyasar Najeriya ta nuna zurfin kishinta kan samar da ingantacciyar al’umma da sadaukarwarta ga hidimar jama’a."
"Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalanta, abokanta, gwamnati da al’ummar jihar Ogun, musamman mazabar Ikenne/Sagamu/Remo ta Arewa da kuma dukkan mambobin majalisar kasa."

- Akin Rotimi

Muƙaman da marigayiyar ta rike a Majalisa

Adewunmi Onanuga, wadda aka fi sani da Ijaya, an haife ta a ranar 2 ga Disamba, 1965 wacce a karon farko aka zabe ta majalisar a shekarar 2019 karkashin jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi raddi ga Sanusi II kan sukar tsare tsaren Tinubu

Marigayiyar kafin rasuwarta ta shugabanci kwamitin majalisar kan harkokin mata da ci gaban zamantakewa a Majalisar.

Bayan zabenta karo na biyu a shekarar 2023, an nada marigayar a matsayin mataimakiyar mai tsawatarwa a Majalisar ta 10.

Yawan 'yan Majalisa ta 10 da suka rasu

"Yayin da muke alhinin rasuwar wannan ‘yar majalisar mai himma da rikon amana, za a ci gaba da tunawa da sadaukarwarta wajen inganta rayuwar al’umma."

- Cewar sanarwar

Bayan rasuwar marigayar, Majalisar Wakilai ta 10 ta rasa mambobi hudu kenan tun bayan kaddamar da ita a watan Yunin 2023 bayan zaɓe.

Mahaifiyar tsohon shugaban Majalisa, Bankole ta rasu

A baya, kun ji cewa mahaifiyar tsohon shugaban majalisar wakilai, Dimeji Bankole, ta yi bankwana da duniya bayan fama da rashin lafiya.

Dattijuwar mai suna Monsurat Bankole, ta rasu ne a ranar Juma’a 10 ga watan Janairun 2025 bayan shafe rayuwarta kan tafarkin addini.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanata, Shehu Sani ya fadi silar lalacewar lamura a Najeriya

Monsurat Bankole ita ce Iya Adinni a yankin Egba, kuma ta kafa kungiyar Al Mönsur Islamic Society wacce ta ba da gudunmawa sosai ga ci gaban addinin Musulunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.