'Sarki 1 ne a Kano': Fitaccen Lauya a Najeriya Ya Yi Bayanin Hukuncin Kotu

'Sarki 1 ne a Kano': Fitaccen Lauya a Najeriya Ya Yi Bayanin Hukuncin Kotu

  • Babban lauya, Femi Falana, ya bayyana cewa Malam Muhammadu Sanusi II ne kadai halattaccen Sarkin Kano
  • Falana ya jaddada cewa tsarin sarauta ba batu ne na kare hakkokin dan adam ba kuma kotun tarayya ba ta da hurumi
  • Babban lauyan ya ce lallai kuma tilas ya kasance Sarki guda daya ne kawai a Kano don guje wa rikice-rikice da rudani

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Lauyan mai fafutukar kare hakkin dan adam, Femi Falana, SAN, ya bayyana cewa dole ne a samu Sarki daya a Kano kamar yadda hukuncin Kotun Daukaka Kara ya zartar. Femi Falana SAN ya dage cewa Malam Muhammadu Sanusi II, wanda ke matsayin Sarki na 16 na Kano, zai ci gaba da zama a kan gadon mulki duk da kokarin jayayya daga wasu.

Kara karanta wannan

Sanatan Arewa ya faɗawa gwamnatin Tinubu dabarar murƙushe ƴan ta'adda cikin sauƙi

Sanusi
Falana SAN ya ce Sanusi ne Sarkin Kano Hoto: Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Falana ya bayyana haka ne a lokacin bikin tunawa da Makarantar Gani Fawehimi da aka gudanar a Lagos, inda ya yi bayani sosai a kan hukuncin.

Femi Falana ya taya Sarki Sanusi II murna

A cewar jaridar Daily Post, fitaccen babban lauya a Najeriya, Femi Falana, ya tabbatar wa Sarki Muhammadu Sanusi II cewa ya yi nasara a kotu na ya ci gaba da zama a karagarsa. Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A matsayinmu na lauyoyi, lokacin da muka hadu, dole ne mu fada wa kanmu wasu gaskiya. Mai Martaba, muna taya ka murna bisa nasarar da ka samu a Kotun Daukaka Kara."

Falana ya yi hasashe kan rikicin masarautar Kano

Femi Falana SAN ya bayyana cewa babu yadda masu adawa da Sarautar Sarki Sanusi II za su yi illa su nufi tafi kotun koli a fafutukar su na kawo karshen mulkinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bugi karji kan darajar Afrika a Qatar, ya fadi sirrin cigaban nahiyar

Falana SAN ya ce:

"Masu adawa da kai suna cewa za su tafi Kotun Koli, kuma bisa la'akari da doka, wannan haka ya ke, kuma a nan ne Hukumar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ya kamata ta shigo
"Doka ta bayyana cewa tsarin sarauta ba batu ne na hakkokin dan adam ba. Saboda haka, ba za a iya cewa a matsayin wani mai sarauta, za ka tafi kotu don kare hakkokin dan adam ba.
"Hakazalika, kotu ta tabbatar da cewa Kotun Tarayya ba ta da hurumin yanke hukunci kan al’amuran masarautar.
"Saboda haka, idan wasu daga cikin abokan aikinmu suna yaudarar kwastomominsu kuma suna jawo matsala a kasar, NBA na da hakkin shiga, ta kuma yi wa abokan aikinmu jagora.”

"Kai ne Sarkin Kano," Falana ga Sanusi II

Lauya Femi Falana ya ce babu wani abin da zai kawo karshen mulkin Muhammadu Sanusi II a kujerar da gwamnatin Kano ta mallaka masa a yanzu. Ya ce abin da ya dace shi ne kungiyar lauyoyi ta kasa ta yi kokarin warware hukuncin yadda za a kawo karshen turka-turka a masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Lauya ya fadi hanyar da ta ragewa Aminu Ado bayan nasarar Sanusi II a kotu

Lauya ya fadi wanene Sarkin Kano

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Kwamishinan shari’a na jihar Kano, M.A. Lawan, ya yi bayanin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara kan rikicin masarautar Kano.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, M.A. Lawan ya zargi gwamnatin jihar Kano da yin kuskuren fassara hukuncin kotun, inda ta ke bayyana Muhammadu Sanusi a matsayin Sarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.