Sojoji da 'Yan Sanda Sun Gwabza da Masu Neman Raba Najeriya, An Kashe Miyagu
- Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a Jihar Anambra ta kashe ’yan ta’adda biyar yayin wani samame a sansanin ’yan a ware a kauyen Ufuma
- Jami'an tsaro sun gano bindigogi, na’urar tashin bam da wasu kayayyaki masu alaka da aikata laifi a sansanin kafin rushe shi
- Kwamishinan ’yan sandan jihar ya bukaci hadin kan jama’a wajen yakar miyagun mutane da dawo da zaman lafiya a yankin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Anambra - A wani samame da aka kai a ranar 14 ga watan Janairu, 2025, jami’an tsaro na hadin gwiwa sun samu nasarar kashe ’yan ta’adda biyar.
Ana zargin 'yan ta'addar suna da hannu a aikata laifuffuka a kauyen Ufuma, karamar hukumar Orumba ta Arewa, Jihar Anambra.
Rundunar 'yan sandan jihar ta wallafa yadda ta samu nasarar kutsawa maboyar 'yan ta'addar a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana ganin nasarar ta kara karfafa yaki da rashin tsaro tare da jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro a jihar.
Yadda aka gano makaman 'yan a ware
Jami’an tsaro sun samu nasarar kai wannan farmakin ne a yankin Umugem, a cikin Ufuma, da misalin karfe 12:30 na rana.
A yayin samamen, rundunar ta kashe ’yan ta’adda biyar da ake zargi suna cikin masu fafutukar raba Najeriya yayin da wasu suka tsere dauke da raunukan harsashi.
An gano abubuwa masu hadari da suka hada da na’urar tashi bam guda hudu da ba a tayar da su ba, bindigogi biyu kirar AK47 da wasu makaman.
Leadership ta wallafa cewa jami’an tsaron sun rusa sansanin miyagun, wanda ake zargi da zama cibiyar shirya hare-hare da haddasa fitina.
Kokarin kama sauran 'yan a ware
Bayan nasarar samamen, jami’an tsaro sun bayyana cewa suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda suka tsere daga sansanin.
Hukumomin tsaron sun yi kira ga jama’ar yankin su bayar da hadin kai ta hanyar bayar da bayanai masu amfani domin kawo karshen ayyukan miyagun mutane a yankin.
Kiran kwamishinan 'yan sanda ga jama'a
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Anambra, CP Nnaghe Obono Itam ya yi kira ga jama’a da su ba da goyon baya wajen yakar miyagun mutane da dawo da zaman lafiya a yankin.
CP Nnaghe Obono Itam ya ce;
“Dole ne jama’a su hada kai da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa ba a bari wadannan ’yan ta’addan su samu damar ci gaba da haddasa tashin hankali ba.”
Kwamishinan ya kara da cewa duk wanda ke da bayanai kan maboyar ’yan ta’addan da suka tsere ya tuntubi jami’an tsaro cikin gaggawa.
An kama wanda ya kashe 'yar NYSC
A wani rahoton, kun ji cewa yan sandan jihar Nasarawa sun kama matashin da ake zargi ya kashe budurwarsa mai hidimar kasa.
Yayin da ake masa tambayoyi, matashin ya ce budurwar tana hulda da wasu maza kuma bai yi nadamar daukar matakin kashe ta ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng