Gwamna Ya Dakatar da Hadimarsa Nan Take, Ana Zargin Ta Karɓi Kuɗi Masu Nauyi

Gwamna Ya Dakatar da Hadimarsa Nan Take, Ana Zargin Ta Karɓi Kuɗi Masu Nauyi

  • Gwamnan Delta ya dakatar da mataimakiyarsa ta musamman, Favour Obakoro (Vida Modelo), saboda zarge-zargen damfara da ake yi mata
  • An zarge ta da amfani da mukaminta wajen karɓar kuɗi daga mutane ta hanyar yaudara, har ma tana tsoratar da waɗanda suka nemi a maido masu da kudinsu
  • Gwamnatin jihar ta sanar da cewa dakatarwar za ta bai wa hukumomi damar gudanar da cikakken bincike don gano gaskiyar lamarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya dakatar da mai taimaka masa ta musamman kan harkokin ladabi da ƙasashen waje, Favour Obakoro, wadda aka fi sani da Vida Modelo.

Gwamna Sheriff Oborevwori ya dakatar da hadimar tasa ne bisa zargin damfarar mutanen kuɗaɗe wanda ya saɓawa dokar aiki kuma matakin zai fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

2027: Rikici ya barke tsakanin gwamnan Bauchi da ministan Tinubu

Gwamnan Delta.
Gwamnan jihar Delta ya dakatar da hadiminsa kan zargin damfarar kudade Hoto: Sheriff Oborevwori
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta tattaro cewa dakatarwar na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin Delta, Dakta Kingsley Emu, ya fitar ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Oborevwori ya dakatar da hadimarsa

A cewar sanarwar, matakin ya zama dole don bai wa hukumomin tsaro da masu yaƙi da cin hanci da rashawa damar gudanar da bincike mai zurfi kan zarge-zargen da ake yi wa Obakoro.

An zarge ta da amfani da matsayinta na gwamnati wajen karɓar kuɗi masu nauyi daga hannun mutane ta hanyar yaudara.

Wannan abu da ake zargin hadimar gwamnan ta aikata ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta da cikin al’umma a jihar Delta.

Wane laifi hadimar gwamnan ta aikata?

Bincike ya nuna cewa wani shahararren a kafafen sada zumunta, mai suna Very DarkMan, shi ne ya fara fallasa zarge-zargen da ake yi wa hadimar gwamnan.

Very DarkMan ya bayyana cewa mutane da dama daga Delta sun kai masa ƙorafe-ƙorafe, suna zargin cewa Obakoro ta yaudare su ta hanyar yin amfani da ofishinta.

Kara karanta wannan

Gwamna ya daina ɓoye ɓoye, ya fadi manufar sojojin da suka kashe bayin Allah a Zamfara

Har ila yau, ya fitar da hujjoji da suka haɗa da adadin kuɗaɗen da ake zargin ta karɓa daga mutanen da ta damfara.

Wasu daga cikin waɗanda suka yi ƙorafi sun bayyana cewa Obakoro tana amfani da ofishinta wajen tsoratar da su idan suka nemi a maido musu da kuɗinsu.

Wannan hali ya jawo damuwa ga al’umma, musamman yadda ta yi amfani da matsayin da aka bata na gwamnati wajen cutar da jama’a maimakon taimaka musu.

Gwamnatin Delta ta fara bincike kan lamarin

Sanarwar sakataren gwamnati ta bayyana cewa gwamnatin Delta za ta bai wa hukumomin tsaro goyon baya domin tabbatar da cewa an gudanar da bincike cikin adalci.

Gwamnatin ta yi kira ga al’umma su kasance masu bin doka da oda yayin da ake kan gudanar da bincike, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamna Oborevwori ya kori kwamishina

Kun ji cewa Gwamna Sheriff Oborevwori ya sallami kwamishinan yaɗa labarai na jihar Delta, Dokta Ifeanyi Osuoza daga aiki.

Kara karanta wannan

"Ina da mafita amma ba zan taimaka ba," Sarki Sanusi II ya yi wa Shugaba Tinubu tatas

Gwamnan ya naɗa wanda zai rike ma'aikatar yaɗa labaran na wucin gadi kafin naɗa sabon kwamishina, ba a bayyana dalilin korar Dr. Ifeanyi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262