'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Ci Gaba da Ta'addanci a Borno, Sun Yi Barna Mai Yawa

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Ci Gaba da Ta'addanci a Borno, Sun Yi Barna Mai Yawa

  • Mutane da dama sun tafka asara bayan ƴan ta'addan Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci a jihar Borno
  • Ƴan ta'addan a yayin harin da suka kai a wani ƙauye na ƙaramar hukumar Chibok, sun ƙona gidaje da wata coci
  • Mazauna yankin sun koka kan ƙaruwar kai hare-haren da ƴan ta'addan suke yi kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Chibok ta jihar Borno.

Ƴan ta'addan na Boko Haram sun kai harin ne a ƙauyen Shikarkir da ke ƙaramar hukumar Chibok ta jihar Borno.

'Yan Boko Haram sun kai hari a Borno
'Yan ta'addan Boko Haram sun kona gidaje da coci a Borno Hoto: @ProfZulum
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mayaƙan na Boko Haram sun ƙona coci da wasu gidaje a yayin harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan sun farmaki wani ƙauyen Chibok, mai suna Bamzir, suka kashe mutane biyu tare da ƙona wata coci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi magana kan kisan manoma 40, ta fadi abin da ya faru

Ƴan sanda sun yi magana kan harin Boko Haram

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da harin da aka kai Bamzir, amma ya ce bai samu cikakken bayani game da abin da ya faru a Shikarkir ba.

"A ranar 12 ga watan Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 2:00 na dare, ƴan Boko Haram sun kai hari a ƙauyen Bazir da ke Chibok, suka kashe mutane biyu, suka ƙona gidaje fiye da 30 da cocin EYN."
"An ƙara tsaurara tsaro bayan dawo da zaman lafiya. Kwamishinan ƴan sanda ya umarci jami’anmu su tattara bayanan sirri domin fitar da rahoto, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a."

- ASP Nahum Daso

Ƴan Boko Haram na ta'addanci a Borno

Wani wanda harin ya ritsa da gidansa, Malam Daniel Shikarkir, ya ce iyayensa sun tsira ba tare da wani rauni ba.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun mamaye kauye suna harbi, sun kashe manoma 40

"Kwanakin baya, irin wannan al’amari ya auku a wani ƙauyen da ke makwabtaka da mu, wanda ya tilastawa dukkan mazauna yankin tserewa zuwa wuraren da suka fi tsaro."

- Malam Daniel Shikarkir

Wani mutum mai suna Mista Paul Mauntah Yaga, ya koka kan halin rashin tsaro a ƙaramar hukumar Chibok wanda ke ci gaba da ta’azzara.

"Harin da Boko Haram ke kai wa cikin ƴan kwanakin nan ya sanya al’ummarmu cikin tsoro da rashin tabbas."
"A ranar 2 ga watan Janairu, 2025, Boko Haram sun kai hari kan ƙauyen Njiland, kuma abin takaici, hare-haren ba su tsaya ba.
“A ranar 12 ga watan Janairu, 2025, sun kai hari kan Bamzir, inda suka kashe matasa biyu, suka raunata wata mata, tare da ƙona gidaje, shaguna da cocin EYN."

- Mista Paul Mauntah Yaga

Ya ce hare-haren da aka kai wa ƙauyukan Njiland da Shikarkir kwanan nan, abin tayar da hankali ne matuƙa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno, sun yi barna mai yawa

Gwamnatin Borno ta magantu kan harin Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da harin da ƴan ta'addan Boko Haram suka kai, inda suka kashe aƙalla manoma 40.

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum ta jajanta kan harin sannan ta buƙaci jami'an tsaro da su bi sawun miyagun domin cafko su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng