Farashin Litar Mai Zai Haura zuwa N1050 a Jihohin Arewa, IPMAN Ta Bayyana Dalili

Farashin Litar Mai Zai Haura zuwa N1050 a Jihohin Arewa, IPMAN Ta Bayyana Dalili

  • Kungiyar IPMAN ta ce farashin litar man fetur zai zarce N1,000 saboda karin harajin da hukumar NMDPRA ta yi a kwanan nan
  • Shugaban IPMAN ya ce karin farashin man ba daga matatar Dangote yake ba, illa sabon tsarin haraji da NMDPRA ta kakaba
  • Alhaji Salisu Ten Ten ya bayyana cewa farashin man fetur zai kai tsakanin N1,040 zuwa N1,050, musamman a jihohin Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (IPMAN) ta bayyana cewa farashin litar mai zai iya kai wa fiye da N1,000 nan ba da jimawa ba.

IPMAN ta danganta wannan kari ga harajin da hukumar NMDPRA ta sanya, wanda ya zama dole dillalan mai su biya a yanzu.

Shugaban IPMAN na Arewa ya yi bayani game da karin kudin man fetur
IPMAN ta ce za a samu karin kudin man fetur yayin da hukumar NMDPRA ta sanya haraji. Hoto: Bloomberg via Getty Images
Asali: UGC

Harajin NMDPRA ya jawo tsadar man fetur

Alhaji Salisu Ten Ten, shugaban IPMAN na Arewa, ya tabbatar da hakan a wata hira da BBC Hausa yayin bayyana dalilin karin farashin mai.

Kara karanta wannan

Sanatan Arewa ya faɗawa gwamnatin Tinubu dabarar murƙushe ƴan ta'adda cikin sauƙi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, a baya ana shigo da man fetur daga kasashen waje, amma yanzu an dakatar da hakan saboda fara aikin matatar Dangote.

Ya kara da cewa a baya, dillalan da ke shigo da mai suna biyan harajin N10 ga kowacce lita da hukumar NMDPRA ta kayyade.

"Yanzu da aka fara amfani da man fetur daga matatar Dangote, hukumar NMDPRA ta bukaci a ci gaba da biyan wannan haraji."

- Salisu Ten Ten.

Masu rumbuna sun kara kudin dakon mai

Shugaban IPMAN ya ce kafin karin, farashin kowacce lita daga rumbun ajiyar mai yana tsakanin N912 zuwa N913, amma yanzu harajin ya jawo karuwar farashin.

"Masu depot sun bayyana cewa karin N10 akan farashin lita ya sanya dole suma su kara kudin man da suke bawa dillalai.

- A cewar shugaban IPMAN.

Alhaji Salisu Ten Ten ya ce wannan karin farashi daga masu rumbunan ajiyar mai ya tilasta wa masu gidajen mai kara farashin man a gidajensu.

Kara karanta wannan

A karon farko a shekaru 10, Najeriya ta fara shigo da shinkafa daga kasar waje

Abin da ya jawo dillai suka kara farashin mai

Ya ce matatar Dangote ba ta da hannu a wannan karin, domin har yanzu ba ta kara farashin mai ba, illa kawai harajin NMDPRA.

Alhaji Salisu ya ce:

"Dillalai suna siyan kowacce lita akan N935 daga deffo, sannan suna kara kudin lodi da dakon mai, wanda ya janyo karin farashi."

Shugaban 'yan kasuwar man ya ce dole ne dillalai su kara kudi akan farashin su domin su samu riba, wanda ya janyo tsadar mai a kasuwa.

Karin farashin fetur zai fi shafar Arewa

A cewarsa, farashin man fetur a jihohin Arewa zai iya kai wa tsakanin N1,040 zuwa N1,050 saboda yanayin kasuwar yanzu.

Alhaji Salisu ya ce karin farashin ya fi shafar yankunan Arewa, inda kudin jigilar mai da sauran haraji ke kara tsadar litar mai.

Wasu rahotanni sun nuna cewa masu rumbunan ajiyar mai sun riga sun kara farashin litar mai zuwa N950, wanda ke kara matsa lamba ga dillalai.

Kara karanta wannan

Sabuwar matsala: Amurka ta yi abin da ya jawo man fetur ya ƙara kuɗi a duniya

IPMAN ta yi kira ga gwamnati da ta duba wannan karin farashi domin rage matsin da ke damun dillalai da masu amfani da mai a Najeriya.

Farashin fetur ya kara tsada a duniya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, farashin danyen mai ya tashi zuwa $81, mafi girma cikin watanni hudu, sakamakon takunkumin Amurka kan Rasha.

Takunkumin ya sa kasashen China da Indiya sayen mai daga Gabas ta Tsakiya da Afrika, wanda ya kara farashin fetur a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.