CBN Ya Gano Masu Jawo Karancin Kudi, Ya Lafta Musu Tarar Naira Biliyan 1.35

CBN Ya Gano Masu Jawo Karancin Kudi, Ya Lafta Musu Tarar Naira Biliyan 1.35

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ci tarar bankuna tara ta zunzurutun kudi Naira biliyan 1.35 saboda rashin fitar da takardun kudi ta ATM
  • An ruwaito cewa kowanne banki da aka samu da laifi an ci tararsa Naira miliyan 150 saboda saba dokokin raba kudi na bankin CBN
  • CBN ya gargadi bankuna cewa za a ci gaba da sanya ido kan bin dokokin raba kudi domin tabbatar da bin doka da oda a harkokin bankuna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bankin CBN ya ce ya ci tarar bankuna jimillar Naira biliyan 1.35 saboda rashin bin dokokin bayar da kudi ta na’urorin ATM, musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Wannan hukuncin ya biyo bayan bincike da CBN ya gudanar a bankunan domin tabbatar da wadatar kudi a lokacin da ake bukatar su sosai.

Kara karanta wannan

Tinubu ya jaddada shirin ragargazar 'yan ta'adda a fadin Najeriya

CBN Najeriya
CBN ya ci tarar bankuna N1.35bn. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Vanguard ta wallafa cewa CBN ya ce matakin ya nuna karara cewa bankin ba zai lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga yaduwar kudi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankunan da CBN ya hukunta a Najeriya

A jerin bankunan da aka ci tarar akwai Bankin Fidelity, First Bank, Bankin Keystone, Union Bank, Bankin Globus, Bankin Providus, Bankin Zenith, Bankin UBA da Sterling.

CBN ya ci kowanne banki daga cikin su tarar Naira miliyan 150, tare da sanar da cewa za a cire kudin kai tsaye daga asusun ajiyar su na babban bankin.

Punch ta rahoto cewa Daraktan Watsa Labaran CBN, Hajiya Hakama Sidi Ali, ta tabbatar da wannan mataki, tana mai cewa:

“Tabbatar da wadatar kudi yana da muhimmanci wajen samar da kwanciyar hankali ga al’umma.”

Gargadin da CBN ya yi ga bankuna

CBN ya bayyana cewa bankuna sun dade suna samun gargadi kan bin dokokin raba kudi, amma wasu sun gaza bin umarnin, lamarin da ya tilasta daukar matakan ladabtarwa.

Kara karanta wannan

A karon farko a shekaru 10, Najeriya ta fara shigo da shinkafa daga kasar waje

“CBN ba zai yi kasa a guiwa wajen ladabtar da duk wani banki da ya saba dokokin raba kudi ba,”

- Hakama Sidi Ali

Haka zalika, CBN ya kara da cewa zai ci gaba da sa ido kan yadda bankuna ke rike kudi da kuma yadda masu na’urar POS ke amfani da damar su wajen rarraba kudin.

Yemi Cardoso ya yi kira ga bankuna

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya taba jan hankalin bankuna a lokacin wani taro cewa dole ne su bi dokokin raba kudi ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

“Manufarmu ita ce tabbatar da wadatar kudi a kowanne lokaci, domin ci gaban al’umma da karfafa gwiwar jama’a,”

- Olayemi Cardoso

CBN ya yi kira ga bankuna da su tabbatar suna bin dokoki, yana mai gargadin cewa duk wanda ya saba zai fuskanci hukunci nan take.

Maganar amfani da tsofaffin kudi

Kara karanta wannan

Shugaba a APC ya yi zazzafan martani ga El Rufa'i kan hadaka da 'yan adawa

A wani bangare kuma, CBN ya sake jaddada cewa tsofaffin takardun kudin Naira; N1000, N500, da N200 har yanzu suna cigaba da aiki.

A wata sanarwa da Hajiya Hakama ta fitar, CBN ya ce hukuncin Kotun Koli na ranar 29 ga Nuwamban 2023 ya ba da damar ci gaba da amfani da wadannan takardun kudin.

An shigar da bankin CBN kara kotu

A wani rahoton, kun ji cewa ma'aikatan babban bankin CBN da aka sallama daga aiki sun dauki matakin zuwa kotu.

An ruwaito cewa ma'aikatan sun bukaci kotu da ta dakatar da sallamarsu daga aiki da aka yi inda suka ce lamarin ya saba dokar kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng