Obasanjo Ya Kauda Kai kan Bambancin da ke Tsakaninsa da Tinubu, Ya ba Shi Shawara

Obasanjo Ya Kauda Kai kan Bambancin da ke Tsakaninsa da Tinubu, Ya ba Shi Shawara

  • Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya nuna muhimmancin da ilmi yake da shi domin samun ci gaba a ƙasa
  • Obasanjo ya buƙaci gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta samar da kuɗaɗe domin ɗorewar ilmi a Najeriya
  • Tsohon shugaban ƙasar ya kuma buƙaci gwamnatoci a kowane matakai da su ba matasa damar zama masu samar da ayyukan yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ba gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu shawara kan ilmi.

Olusegun Obasanjo ya yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu da ta mayar da hankali kan samar da kuɗaɗe domin ɗorewar ilimi a Najeriya.

Obasanjo ya ba Tinubu shawara
Obasanjo ya bukaci Tinubu ya fifita bangaren ilmi Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta rahoto cewa tsohon shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a jami’ar fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH), da ke Ogbomoso, jihar Oyo, a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya fayyace gaskiya kan sukar Shugaba Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban ƙasan ya je jami'ar ne domin halartar bikin cika shekaru 70 na shugaban jami’ar Bells, Oludele Ojediran.

Wace shawara Obasanjo ya ba Tinubu?

Obasanjo ya jaddada buƙatar gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa ilimi ya ci gaba da zama ginshiƙin cigaban ƙasa, rahoton The Guardian ya tabbatar.

“Shugaba Tinubu da gwamnatin tarayya dole ne su nemo hanyoyin samar da kuɗaɗe domin dorewar ilimi."
"Dole ne gwamnati ta duk matakai, ta ba matasa damar zama masu samar da ayyukan yi."

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya yabawa jami'ar LAUTECH saboda gudunmawar da take bayarwa wajen kyautata harkokin ilimi.

Ya jinjinawa jami’ar saboda samar da shugabanni nagari, ciki har da Farfesoshi irinsu Adeyemi da Ojediran, waɗanda dukkansu sun taɓa riƙe muƙamin shugaban jami’ar Bells.

Tsohon shugaban ƙasan ya sake jaddada ra’ayinsa na cewa a samar da ilimi don amfani ba don riba ba, yana mai tabbatar da jajircewarsa wajen ci gaba da bunƙasa harkar ilimi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fadi abin da ya aikata Abacha ya tura shi kurkuku

Basarake ya yabawa tsohon shugaba Obasanjo

A nasa ɓangaren, Soun na Ogbomoso, Oba Ghandi Olaoye, ya yabawa gudunmawar da Obasanjo ya bayar a ɓangaren ilimi da aikin gona a ƙasar nan.

Da yake jawabi ga Farfesa Ojediran, basaraken ya buƙace shi da ya yi amfani da ƙwarewarsa a fannin aikin injiniyan noma domin bunƙasa aikin gona a Ogbomoso.

Oba Ghandi Olaoye ya jaddada aniyarsa ta inganta ci gaban aikin gona a yankin Ogbomoso da kewaye.

“Zan bayar da fili da ya dace don noma ga duk wanda yake sha’awar aikin gona a Ogbomoso da kewaye,”

- Oba Ghandi Olaoye

Obasanjo ya caccaki kamfanin NNPCL

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya caccaki kamfanin mai na Najeriya (NNPCL) kan gayyatar da ya yi masa ya duba matatun man da aka gyara.

Obasanjo ya bayyana gayyatar a matsayin cin mutunci ga ofishinsa domin kamfanin NNPCL bai aika masa da wasiƙa a hukumance ba kan gayyatarsa zuwa rangadin gani da ido a matatun man.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng