Gwamnoni 6 Sun Ajiye Siyasa Gefe, Sun Ɗauki Matakin Kare Jihohinsu daga Ƴan Ta'adda

Gwamnoni 6 Sun Ajiye Siyasa Gefe, Sun Ɗauki Matakin Kare Jihohinsu daga Ƴan Ta'adda

  • Jihohin Kudu maso Yamma sun fara shirin magance rahoton shigowar miyagun mutane daga Arewa zuwa dazukan yankin
  • An ce DSS ta kama mutum 10 da ake zargin ‘yan ISWAP ne, yayin da gwamnonin yankin suka fara tuntuɓar juna kan tsaro
  • Kungiyar OPC ta yi kira ga gwamnonin da su dauki matakan tsaro na gaggawa, domin kare al'umma daga barazanar ‘yan ta’adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Jihohin yankin Kudu maso Yamma sun fara shirin magance rahoton shigowar ‘yan bindiga da ‘yan ISWAP zuwa dazukan yankin.

Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya gargadi jama’a cewa ‘yan ta'adda daga Arewacin Najeriya suna kokarin samun mafaka a jihar.

Gwamnonin Kudu maso Yamma sun yi magana kan sha'anin tsaron yankinsu
Gwamnonin Kudu maso Yamma sun dauki matakan kare jihohinsu daga ISWAP. Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

"Yan ta'adda na shigowa Oyo daga Arewa" - Makinde

Ya bayyana haka ne yayin wani taron addinai na shekara-shekara da aka shirya a garin Agodi da ke birnin Ibadan, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Cire tallafin fetur ya fara haifar da sauƙi ga talakawa, cewar hadimin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makinde ya ce:

"Na samu rahoton tsaro cewa wasu miyagun mutane daga Arewa maso Yamma na kwarara zuwa nan jiharmu saboda luguden sojoji.
"Za mu nemo su, kuma za mu dauki matakan da suka dace don kare jiharmu daga barazanar tsaro."

Gwamnatin Ogun ta ce ta tuntuɓi hukumomin tsaro, ciki har da sojoji da ‘yan sanda don daukar matakan tsaro.

OPC ta nemi gwamnoni su dauki matakin gaggawa

Hukumar DSS ta kama wasu mutum 10 da ake zargin ‘yan kungiyar ISWAP ne a Ilesa, jihar Osun.

DSS ta nemi umarnin wata kotun tarayya don tsare wadanda ake zargi tsawon kwana 60, kuma kotu ta amince.

A wannan gabar ne kungiyar OPC ta yi kira ga gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma da su dauki batun tsaro a matsayin wani abu na ujila.

Ta kuma ba da tabbacin cewa za ta taimaka wa hukumomin tsaro wajen magance barazanar ‘yan ta’adda a shiyyar.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya farmaki masallaci a Zamfara, ya yi garkuwa da masu ibada

Gwamnan Legas ya ba da tabbaci kan tsaro

Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma ya ce yana tuntuɓar takwarorinsa na yankin kan batun tsaro.

Mai bai wa Sanwo-Olu shawara kan watsa labarai, Gboyega Akosile, ya ce gwamnan na karbar bayanan tsaro kullum daga sassa daban-daban.

Akosile ya ce duk da babu tabbacin ainihin kasancewar ‘yan bindiga a yankin, hakan ba zai sa su yi sakaci ba kan batun tsaron.

Gwamnonin yankin sun shirya taro

Ya kuma kara da cewa a taron farko na gwamnonin Kudu maso Yamma, an mayar da hankali ne kan tsaron yankin.

Gwammnonin yankin sun shirya tattaunawa kan hanyoyin magance barazanar tsaro cikin yankin.

Wannan taron zai zama wata hanya ta tabbatar da an dauki matakan kare lafiya da dukiyoyin al’ummar yankin daga 'yan ta'adda.

'Yan ta'adda sun farmaki kwamishina

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu ‘yan ta’adda sun farmaki kwamishinan muhallin jihar Oyo, Mogbanjubola Olawale, yayin aikin tsaftar muhalli a Mobil, Ibadan.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin Arewa sun sake bijerewa kudirin haraji, sun fadi illarsa ga talaka

Rahoto ya bayyana cewa harin 'yan ta'addar ya jikkata wasu ‘yan tawagar Olawale, inda aka kai su asibiti, yayin da motocinsu suka lalace.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.