Sanata Ndume Ya Fayyace Gaskiya kan Sukar Shugaba Bola Tinubu
- Sanata Ali Ndume ya yi magana kan caccakar da yake yi wa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Ali Ndume ya bayyana cewa ba ya sukar shugaban ƙasan, sai dai manufofinsa domin yana matuƙar ganin girmansa
- Sanatan ya shawarci Shugaba Tinubu da maida hankali wajen aiwatar da kasafin kuɗi ta yadda ƴan Najeriya za su amfana
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Kudancin Borno, Ali Ndume, ya yi magana kan sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Ndume ya bayyana cewa yana matuƙar ganin girman Shugaba Bola Tinubu, wanda hakan ba zai bari ya zama mai suka a gare shi ba.
Sanata Ndume ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar talabijin ta Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndume ya musanta sukar Tinubu
Ali Ndume ya ƙaryata zargin cewa yana gaba da Shugaba Tinubu, yana mai cewa sukar da yake yi yana yin ta ne a kan manufofin shugaban ƙasan.
Sanata Ndume ya kasance mai bayyana ra'ayinsa kan halin matsin tattalin arziƙi a ƙasar nan a ƙarƙashin Tinubu, inda ya jaddada cewa masu ba shugaban ƙasa shawara, ba su ba shi mai kyau.
"Ba na sukar shugaban ƙasa, sai dai manufofinsa. Ba na adawa da wannan gwamnati ba, gwamnatin mu ce."
"Ba na caccakar na gaba da ni, ni ɗan soja ne, kuma a bariki muna girmama na gaba da mu. Tinubu na gaba da ni ne, kuma ina girmama shi, amma ina samun saɓani da shi a wasu wurare, amma da fatan za mu yi daidaito a wasu wuraren."
- Sanata Ali Ndume
Menene dalilin haɗuwar Ndume da Tinubu?
Sanata Ndume ya kuma yi magana kan wani hoto da ya karaɗe kafafen sada zumunta da ke nuna shi tare da Tinubu cikin farin ciki.
"Yana yawan cewa ba na zuwa fadar shugaban ƙasa. Na ce masa bai taɓa gayyata ta ba, sai ya ce zan iya zuwa da daren nan."
"Sannan ya ce zai halarci bikin auren ƴata, duk da cewa ya yi karo da bikin tunawa da sojojin Najeriya. Bayan bikin, ina tsammanin zai tafi, amma sai ya ce ba zai je ko’ina ba, zai tsaya domin auren. Wannan shi ne abin da ya faru."
- Sanata Ali Ndume
Ndume ya ba Tinubu shawara
Da yake magana kan hanyoyin magance manyan matsalolin ƙasar nan, Ndume ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya maida hankali kan aiwatar da kasafin kuɗi tare da ba da muhimmanci ga ɓangarorin tsaro da jin daɗin jama'a.
"Na sha gayawa shugaban ƙasa ya aiwatar da kasafin kuɗi, ƴan Najeriya za su yi farin ciki. Ya maida hankali kan abubuwa biyu, tsaro da jin daɗin jama'a."
- Sanata Ali Ndume
Tinubu ya yi naɗi a hukumar DSS
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi sabon naɗi a hukumar tsaron farin kaya ta DSS.
Shugaba Tiinubu ya ɗauko ƴar asalin jihar Kogi da ke yankin Arewa ta Tsakiya ya ba ta muƙamin mataimakiyar darakta janar ta hukumar DSS.
Asali: Legit.ng