Shugaba Tinubu Ya Kafa Tarihi, Ya Yi Muhimmin Nadi a Hukumar DSS

Shugaba Tinubu Ya Kafa Tarihi, Ya Yi Muhimmin Nadi a Hukumar DSS

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da yin sabon naɗi a hukumar tsaron farin kaya ta DSS
  • Mai girma Bola Tinubu ya amince da naɗin ƴar asalin jihar Kogi, Folashade Arinola Adekaiyaoja, a matsayin mataimakiyar darakta janar ta DSS
  • Naɗin da aka yi wa Folashade ya samu yabo daga wajen ma'aikatan hukumar waɗanda suka yi ritaya da masu aiki a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sabon naɗi a hukumar tsaron farin kaya ta DSS.

Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Folashade Arinola Adekaiyaoja fsi+, fdc, a matsayin mataimakiyar darakta janar ta hukumar DSS.

Tinubu ya yi nadi a hukumar DSS
Tinubu ya amince da nadin mataimakiyar darakta janar a hukumar DSS Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya yi naɗi a hukumar DSS

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa naɗin da Shugaba Tinubu ya yi, shi ne irinsa na farko da wani shugaban ƙasa ya taɓa yi a tarihi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare hanya, sun yi awon gaba da sojoji, fasinjoji masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naɗin da aka yi wa Folashade Arinola ya samu yabo daga ma’aikatan DSS na yanzu da kuma waɗanda suka yi ritaya.

Wasu na ganin wannan naɗin da aka yi mata, a matsayin wanda aka yi shi ne don dawo da ƙwarewa da cancanta a cikin aikin hukumar.

Rahotanni sun nuna cewa amincewar shugaban ƙasar ta yi daidai da shirin sake fasalin tsarin hukumar domin samar da ingantaccen aiki, bisa tsarin asali na hukumar.

Bincike ya nuna cewa DSS tana da tsarin da ya kunshi mataimakan darakta janar guda uku a cikin jerin mukaman shugabancinta.

Yadda Folashade Arinola ta zama DG DSS

Naɗin Folashade Arinola Adekaiyaoja, wanda shugaban ƙasar ya amince da shi, ya biyo bayan shawarar da darakta janar na DSS ya gabatar ta hannun mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Mallam Nuhu Ribadu.

Wata majiya ta bayyana cewa wannan naɗin ya yi daidai da ƙa’idojin hukumar, kuma ya kasance abu ne wanda bai taɓa faruwa ba a tarihin hukumar DSS.

Kara karanta wannan

Cire tallafin fetur ya fara haifar da sauƙi ga talakawa, cewar hadimin Tinubu

Ma'aikatan DSS na murna da naɗin Tinubu

Naɗin Folashade Arinola Adekaiyaoja wacce ƴar asalin jihar Kogi ce, ya samu ƙarbuwa sosai a tsakanin ma’aikatan hukumar DSS.

Ma'aikatan na DSS sun yi amanna cewa tana da cikakkiyar cancanta don riƙe wannan matsayin da aka bata.

Shugaba Tinubu bisa alƙawarin da ya yi na inganta tsaro da dukiyoyin ƴan Najeriya, ya umurci shugabannin hukumomin tsaro da su gabatar da shawarwari kan yadda za a inganta ayyukansu.

Darakta Janar na DSS, Mista Oluwatosin Ajayi, tun lokacin da ya kama aiki a ƙarshen watan Agusta na shekarar 2024, ya yi alkawarin kawo sauye-sauyen da za su mayar da DSS zuwa daya daga cikin manyan hukumomin tsaro na sirri a duniya

Shugaba Tinubu ya samu goyon baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanu tagomashi a yunƙurin da yake yi na sake tsayawa takara a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa mai sukar kudirin harajin Tinubu ya sauya ra'ayi, ya fadi dalili

Ƙungiyar ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo ta fito ta nuna goyon bayanta kan Bola Tinubu ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng