'Yan Bindiga Sun Tare Hanya, Sun Yi Awon Gaba da Sojoji, Fasinjoji Masu Yawa

'Yan Bindiga Sun Tare Hanya, Sun Yi Awon Gaba da Sojoji, Fasinjoji Masu Yawa

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun ɗana tarko kan matafiya a jihar Kogi da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Ƴan bindigan waɗanda suka yi wa matafiyan kwanton ɓauna sun sace mutum 33 ciki har da waau jami'an tsaro na sojoji
  • Miyagun dai sun saba yin ta'asa a hanyar wacce ta haɗa yankin Arewa ta Tsakiya da jihar Enugu da ke a Kudu maso Gabashin Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane 33, ciki har da sojoji uku, a jihar Kogi.

Ƴan bindigan sun sace mutanen ne a ƙauyen Ogugu da ke ƙaramar hukumar Olamaboro, ta jihar Kogi.

'Yan bindiga sun sace matafiya a Kogi
'Yan bindiga sun sace sojoji a Kogi Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a kan titin Enugu-Ezike-Kogi, wanda ya haɗa jihar Enugu da yankin Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun mamaye kauye suna harbi, sun kashe manoma 40

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka sace fasinjoji da sojoji

Shaidu sun bayyana cewa ƴan bindigan, waɗanda adadinsu ya kai kusan 17, sun yi kwanton ɓauna ne a wani ɓangaren da ya lalace na hanyar, inda suka tilastawa fasinjojin shiga cikin daji.

Cikin waɗanda aka sace har da sojoji huɗu da ke tafiya daga Akwa Ibom zuwa Kaduna a ɗaya daga cikin motocin haya.

Wani shaidar gani da ido da ya bayyana abin da ya faru, ya ce ƴan bindigan sun daɗe suna cin karensu babu babbaka a hanyar.

"Masu garkuwar sun yi aiki na kusan awa ɗaya. Sun kai hari kan motoci guda uku masu kujeru 18-18, inda suka tilasta aƙalla fasinjoji 35 shiga cikin daji."
"Ɗaya daga cikin sojojin da ya tsere ya faɗa mana cewa suna kan hanyarsu ta zuwa jihar Kaduna ne lokacin da harin ya faru."

- Wani shaida

Ƴan bindiga sun yi ta'asa

Kara karanta wannan

Bello Turji na tsaka mai wuya, sojojin Najeriya sun yi wa yaransa ruwan wuta a Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun harbe ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, wanda ya kasa ci gaba da tafiya saboda rauni.

Daga baya, mafarauta da sojoji sun gano gawarsa a cikin daji a lokacin da suka bi sawun miyagun ƴan bindigan.

Irin makamancin wannan lamarin ya faru a yankin a ranar 24 ga watan Disamba, 2024, lokacin da wasu masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da mutane 31 da ke cikin motocin haya guda huɗu.

Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa a lamarin na ranar 24 ga Disamba, 2024, Onyinyechi Ugwuoke, ta tabbatar da cewa an biya kuɗin fansa, kafin ta samu ƴanci a ranar 28 ga Disamba, 2024.

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Imo

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsagerun ƴan binɗiga sun kai hare-hare a wasu ƙauyukan ƙaramar hukuma Orsu ta jihar Imo.

Ƴan bindigan waɗanda suke ɗauke da makamai sun hallaka mutum 18 a hare-haren na ta'addanci da suka kai a ƙauyukan a cikin rana ɗaya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun far wa jami'an tsaro, sun hallaka sama da 20 a jihar Katsina

Rundunar ƴan sandan jihar Imo, ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng