"Ba Ka da Bakin Sukar Tinubu," Malamin Musulunci Ya Caccaki Gwamnan Bauchi

"Ba Ka da Bakin Sukar Tinubu," Malamin Musulunci Ya Caccaki Gwamnan Bauchi

  • Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya zargi Gwamna Bala Muhammed da sukar kudirin harajin saboda saboda son rai
  • Malamin ya zargi gwamnan Bauchi da wasu malamai da amfani da dokokin haraji da rikicin Najeriya da Nijar don cimma ribar siyasa
  • Gwamna Bala Mohammed ya na daga cikin na gaba a gwamnonin da ke sukar manufofin gwamnatin tarayya a kan talakawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi - Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, fitaccen malamin addinin Islama daga Bauchi, ya zargi Gwamna Bala Muhammed da rashin rashin iya tafiyar da jiharsa.

Malamin ya kara da cewa bai dace gwamna Bala Mohammed ya samu bakin da zai soki manufofin gwamnatin tarayya ba, musamman kudirin haraji.

Tinubu
Dutsen Tanshi ya caccaki gwamnan Bauchi Hoto: Senator Bala Mohammed/Dutsin Tanshi Majlis/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A cikin bidiyon da Dada Olusegun, hadimin Shugaban kasa Bola Tinubu, ya wallafa a shafin X, Idris ya caccaki gwamnan bisa yadda ya dage wajen sukar gwamnatin Tinubu,.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya kafa ma'aikata domin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bala Mohammed ya na daga cikin na gaba-gaba a gwamnonin Arewacin kasar nan da ke adawa da kudirin gyaran haraji da ke gaban majalisa.

Dutsen Tanshi ya caccaki gwamnan Bauchi

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, ya ce Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, ba shi da hurumin yin sukar Shugaba na kasa.

Malamin ya kawo misali da yadda gwamnan ya ware Naira miliyan 400 don sayen kwamfutoci guda shida ga ofishin Sakataren gwamnatinsa.

Malam Idris, wanda ya dade yana fama da rashin lafiya, ya bayyana a cikin wani bidiyo inda ya ce ya na bibiyar muhawarar kan dokokin sauyin haraji da kuma rikicin Najeriya da Nijar.

Dutsen Tanshi ya soki gwamnoni da malamai

Idris Abdulaziz ya zargi Gwamna Bala Muhammed da wasu daga cikin malamai da amfani da dokokin haraji da rikicin da ke tsakanin Najeriya da Nijar domin cimma ribar siyasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bauchi ta soki martanin hadimin Tinubu kan batun kudirin haraji

Malamin ya bayyana cewa maganganun gwamnan game da dokokin haraji siyasa ne, kuma ya yi kira ga al’umma da su guji daukar maganganun gwamnan da muhimmanci.

Gwamna Bala Muhammed ya yi ikirarin cewa dokokin haraji gwamnatin Tinubu za su cutar da Arewacin kasar nan, musamman wajen kara talauta yankin.

Malami ya zargi gwamnatin Bauchi da kwace fili

Malamin ya kara da cewa, maganganun gwamnan kan dokokin haraji ba su da alaka da kishin kasa ko son ci gaban kasa, illa dai yana neman wata dama ta siyasa, kamar kujerar shugaban kasa.

Malamin ya ce;

“Yana amfani da wannan a matsayin dama don samun shugabancin kasa; yana ganin wannan a matsayin wata dama ta cimma abin da yake so ta hanyar yaki da gwamnatin tarayya.”

Gwamnan Bauchi ya fadi dalilin sukar Tinubu

A baya, mun ruwaito cewa wamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana cewa sukar da yake yi wa tsare-tsaren Bola Tinubu ba ta da alaka da siyasa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gama sukar Tinubu, zai kashe N400m don sayen kwamfuta 6

Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa yana goyon bayan kowane tsari da zai kawo ci gaba ga al'umma, kuma yana da hakkin bayar da shawarwari kan tsare-tsaren gwamnatin tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.