Farashin Fetur: Murna za Ta Koma ciki yayin da aka Kara Kudin Dakon Mai

Farashin Fetur: Murna za Ta Koma ciki yayin da aka Kara Kudin Dakon Mai

  • Rahotanni sun nuna cewa manyan rumbunan ajiya sun ƙara farashin fetur daga N908 zuwa tsakanin N950 zuwa N960
  • Karin ya samo asali ne sakamakon tsadar danyen mai a kasuwannin duniya, inda farashin ya kai $79.76 kan kowane ganga
  • Masu dako daga matatar Dangote sun ƙara farashi zuwa N923 kowanne lita, duk da cewa sun ɗauko shi ne a kan N899

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - A ranar Litinin, farashin dakon man fetur da sauran kayayyakin mai da aka tace ya ƙaru a manyan rumbunan ajiya.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan kasuwar mai sun ƙara farashin fetur da dizel a manyan rumbunan ajiya da N43, wanda ya kai ƙarin 4.74%, sakamakon tsadar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun mamaye kauye suna harbi, sun kashe manoma 40

NNPCL
Akwai yiwuwar karin farashin mai Hoto: NNPC Limited/Contributors
Asali: Facebook

A labarin da ya kebanta da Punch, an ruwaito cewa a ranar Lahadi, farashin danyen mai a kasuwar duniya ya kai $79.76 kowanne ganga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan yanayi na nuna cewa gidajen mai na iya ƙara farashinsu domin daidaita da sabon tsadar kayayyakin da aka tace a duniya.

Yadda farashin fetur ya karu a ma’ajiya

Bayanan sun nuna cewa farashin fetur a manyan rumbunan ajiya sun nuna cewa Swift Depot ya ƙara farashinsa zuwa N950 kowanne lita daga N907 a makon da ya gabata.

Haka kuma, Wosbab Depot ya ƙara farashi zuwa N950 daga N909, yayin da Sahara Depot ya ƙara farashinsa zuwa N950 daga N910 da aka siyar a ranar Juma’ar da ta gabata.

‘Yan kasuwa sun kara farashin dauko fetur

Wasu rumbunan masu zaman kansu sun bi sahu wajen ƙara farashi, inda aka gano Shellplux Depot ya ƙara farashin zuwa N960 daga N908.

Chipet Depot ya bukaci ‘yan kasuwa su biya N960 a kowanne lita don karɓar kayansu, wanda a makon da ya gabata ya sayar da shi a kan N908.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun mamaye hedikwatar PDP bayan rikicin jam'iyya ya yi kamari

Nipco Depot ya ƙara farashi da N38, daga N912 zuwa N950, yayin da Matrix Warri Depot ya ƙara farashin daga N925 zuwa N945 kowanne lita.

Masu dakon kayayyaki daga matatar Dangote zuwa sauran ‘yan kasuwa sun ƙara farashi zuwa N923 kowanne lita, duk da cewa sun ɗauko kayan daga matatar a farashin N899 kowanne lita.

An samu karin farashin dauko dizil

Wasu rumbunan ajiya sun ƙara farashin dakon dizil, inda Stockgap Depot ya ƙara farashinsa daga N1,080 zuwa N1,150.

Ibeto Depot ya amince da ƙarin farashi daga N1,050 zuwa N1,150 kowanne lita, yayin da Sahara Depot ya sayar da kaya a kan N1,150 daga N1,045 a makon da ya gabata.

Farashin man fetur zai iya sauka

A wani labarin, kun ji cewa akwai yiwuwar farashin man fetur ya sauka zuwa N500 kowace lita nan ba da jimawa ba duba da cewa matatun mai na Fatakwal da Warri aiki sun dawo aiki.

Kara karanta wannan

Cire tallafin fetur ya fara haifar da sauƙi ga talakawa, cewar hadimin Tinubu

An yi hasashen wannan ci gaba zai ƙara samar da man fetur a cikin gida, wanda hakan zai rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje, kuma ya taimaka wajen saukar farashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.