Gwamnan Bauchi Ya Kafa Ma'aikata domin Kawo Karshen Rikicin Manoma da Makiyaya

Gwamnan Bauchi Ya Kafa Ma'aikata domin Kawo Karshen Rikicin Manoma da Makiyaya

  • Gwamna Bala Mohammed ya kaddamar da kamfen din rigakafin dabbobi na 2025 a karamar hukumar Itas-Gadau, jihar Bauchi
  • Sanata Bala Mohammed ya kafa sabuwar ma’aikata mai kula da harkokin kiwo domin magance rikice-rikicen makiyaya da manoma
  • Gwamnatin Bauchi ta bayyana tsare-tsare da suka hada da samar da dam-dam da wasu ayyukan cigaba domini bunkasa kiwo a jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi ya kaddamar da kamfen din shekara-shekara na rigakafin dabbobi na 2025 a Itas na karamar hukumar Itas-Gadau.

Wannan matakin ya kasance wani muhimmin bangare na kokarin gwamnatinsa na bunkasa samar da abinci da kuma inganta tattalin arziki ta hanyar kiwo.

Gwamnan Bauchi
An kafa ma'aikatar kiwo a jihar Bauchi. Hoto: Lawal Mu'azu Bauchi.
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda taron ya gudana ne a cikin wani sako da hadimin gwamnan, Lawal Mu'azu Bauchi ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bugi karji kan darajar Afrika a Qatar, ya fadi sirrin cigaban nahiyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin taron, gwamnan ya sanar da kafa Ma’aikatar Kiwo, wacce aka samar domin kula da bukatun makiyaya da manoma, tare da inganta samar da kayan masarufi daga dabbobi.

An kafa ma’aikatar kiwo a jihar Bauchi

Gwamnan Bauchi ya bayyana cewa kafa sabuwar ma’aikatar ya nuna cikakken kudurin gwamnatinsa na tallafa wa bangaren kiwo, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen tattalin arzikin jihar.

Sanata Bala Mohammed ya ce;

“Manufofinmu sun dogara ne kan amfani da albarkatun da muke da su, dabbobi da mutane, domin kara samar da abinci mai yawa ga jama’ar jihar Bauchi.”

Gwamnan ya yabi sarakunan gargajiya, shugabannin addini, da hukumomin tsaro saboda rawar da suke takawa a kan zaman lafiya, wanda ke kawo cigaba a bangaren noma da kiwo.

Matakan tallafawa makiyaya da manoma

Gwamnan ya yi kira ga jama’ar jihar Bauchi da su kara mayar da hankali kan noma da kiwo domin samun cigaban tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Wani shugaban karamar hukuma ya sake nada hadimai 130 watanni 6 da nadin mutum 100

Ya kuma sanar da cewa gwamnatin jihar tana aiki tare da kungiyoyin agaji da masu bada tallafi domin samar da dam da sauran muhimman ayyukan cigaba da bunkasa kiwo a jihar.

Domin tabbatar da nasarar kamfen din rigakafin, gwamnan ya umurci shugabannin kananan hukumomi su tabbatar da gudanar da shirin da kuma isar da rigakafin ga dukkan dabbobin jihar.

Jinjina ga gwamnan daga masana

Taron ya samu halartar shahararrun shugabanni ciki har da Sarkin Katagum, Alhaji Umar Faruk II, da kuma shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Bauchi, Alhaji Kabiru Yusuf Tilde.

Shugabannin sun yaba wa gwamnan kan irin tallafin da yake bai wa bangarori daban-daban na al’umma, musamman makiyaya da manoma.

Alhaji Kabiru Yusuf ya ce;

“Wannan shiri zai taimaka wajen rage yaduwar cututtuka a tsakanin dabbobi da kuma bunkasa kiwo wanda zai amfani dukkan al’umma.”

Gwamna Bala ya kammala da bayyana kudurinsa na ganin jihar Bauchi ta zama abin misali a fannin noma da kiwo.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gama sukar Tinubu, zai kashe N400m don sayen kwamfuta 6

Dalilin gwamnan Bauchi na sukar Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Mai girma Bala Mohammed ya bayyana dalilin da ya sanya shi sukan gwamnatin Bola Tinubu.

Sanata Bala Mohammed ya ce yana magana ne domin tunatar da gwamnati a kan nauyin da ke kanta ba wai domin wata manufa ta siyasa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng