Majalisar Legas Ta Lissafa Laifuffukan da Suka Jawo Tsige Shugabanta bayan Shekaru 10

Majalisar Legas Ta Lissafa Laifuffukan da Suka Jawo Tsige Shugabanta bayan Shekaru 10

  • Majalisar Dokokin Legas ta tsige Mudashiru Obasa bisa zarge-zargen almubazzaranci da dukiyar gwamnati da hada 'yan majalisa fada da junansu
  • Mojisola Meranda, mai wakiltar Apapa I, ta maye gurbinsa,ta zama mace ta farko da ta dare kujerar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas
  • Bayan tsige Obasa, jami’an tsaro sun kai dauki, inda suka kama wasu matasa dauke da kayan tsafe-tsafe da ke son shiga majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - 'Yan majalisar dokokin jihar Legas sun bayyana wasu dalilai da suka sanya suka tsige Mudashiru Obasa daga matsayin Kakakin Majalisar.

Sun ce, daga cikin manyan kura-kuran da da ake zarginsa tsohon shugaban majalisar da su har ta kai ga tsige shi sun haɗa da rashin zuwa taro da zaman majalisar a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi kunnen uwar shegu, duk da korafe korafe, za a tabbatar da kudirin haraji

Majalisa
An gano dalilan tsige kakakin majalisar Legas Hoto: Hon. Mudashiru Obasa
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa sauran dalilan da su ka raba Rt. Hon. Obasa da kujerarsa har da yawaita watsi da ra’ayin sauran ‘yan majalisar, da kuma tunzura mambobi su rika rikici da juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Litinin, 'yan majalisar sun tsige Obasa, wanda ke wakiltar Agege, bisa zargin yin almubazzaranci da dukiyar gwamnati.

Yadda majalisar Legas ta nada sabon shugaba

The Nation ta wallafa cewa bayan tsige Mudashiru Obasa, ‘yan majalisar sun naɗa tsohuwar mataimakiyarsa, Mojisola Lasbat Meranda a matsayin sabuwar Kakakin Majalisar.

Raba Obasa da kujerarsa bayan ya shafe shekaru 10 ya na kan ta ya ba Meranda damar zama mace ta farko da ta zama Kakakin Majalisa a tarihin jihar Legas.

Haka kuma Majalisar ta cire Sakataren Majalisar, Olalekan Onafeko, a sakamakon tsige Obasa wanda ake ganin tsohon shugaban ne ya kawo shi majalisar.

'Yan sanda sun mamaye majalisar Legas

Bayan tsige shi, jami’an tsaro na Rapid Response Squad (RRS) na jihar Legas, da kuma 'yan sanda sun mamaye harabar majalisar tare da hana masu ababen hawa da mutane shiga wurin.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa sun tsige kakakin Majalisar dokoki, sun zaɓi mace ta maye gurbinsa

An gano wasu miyagu da suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin majalisar sun shiga hannun jami’an tsaro dauke da kayan tsafi da layu, waɗanda ake zargin magoya bayan Obasa ne.

Yadda aka shirya tsige shugaban majalisa

An tsige Obasa ne bayan wani mamba, Femi Saheed, ya gabatar da kudiri bisa sashe na 92(2)(C) na Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya.

Ya zargi Obasa da rashin iya shugabanci da wasu munanan dabi’u nuna iko fiye da kima, rashin mutunta ra’ayin sauran mambobi, cin zarafi da nuna son kai.

Saheed ya kuma zargi Obasa da tafiyar da mulki ta hanyar kama-karya ba tare da yin amfani da tsarin dimokuraɗiyya ba, wanda ya sa ya gabatar da kudiri na neman tsige shi.

'Yan majalisa sun tsige kakakin majalisa

A wani labarin, mun ruwaito cewa a ranar Litinin, 13 Janairu, 2025, 'yan majalisar dokokin jihar Legas sun tsige Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Mudashiru Obasa, bisa zargin rashin ɗa'a.

Kara karanta wannan

Ndume: Matasan Arewa sun gana da Sanatan APC don dakile kudirin haraji a majalisa

Bayan tsige Obasa, 'yan majalisar sun zaɓi Hon. Mojisola Meranda, mai wakiltar mazaɓar Apapa I, a matsayin sabuwar Kakakin Majalisar da Hon. Fatai Mojeed a matsayin mataimaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.