Tinubu Ya Yi Kunnen Uwar Shegu, duk da Korafe Korafe, Za a Tabbatar da Kudirin Haraji
- Majalisar Dattawa ta shirya gudanar da sauraron ra’ayi kan dokokin gyaran haraji, saboda gabatar da su domin karatu na uku da amincewa
- Bayan tattaunawa mai zurfi da hukumomin gwamnati, an cimma matsaya kan batutuwan da suka shafi gyaran tsarin haraji a Najeriya
- Shugaban FIRS da sauran masu ruwa da tsaki sun tabbatar da cewa dokokin haraji na da muhimmanci, kuma dukkansu sun amince da tsarinsa
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ta caccakar tsarin kudirin musamman daga Arewacin Najeriya, ana ganin zai iya talauta jihohin yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Alamu sun tabbatar da cewa Majalisar Dattawa za ta gudanar da sauraron ra’ayi kan dokokin gyaran haraji, domin gabatar da su a karatu na uku.
An yi wata ganawar sirri tsakanin Kwamitin duba kan kudirin haraji da kuma masu ruwa da tsaki domin samun damar amincewa da kudirin.
An tattauna da jami'an gwamnati kan kudirin haraji
Channels TV ta ce hakan ya tabbata ne bayan zaman sirri na kwamitin rikon kwarya na majalisar da manyan jami’an gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikin wadanda suka halarci ganawar akwai Antoni-janar na Tarayya, Lateef Fagbemi da Shugaban hukumar FIRS, Zacch Adedeji.
Sai kuma Shugaban Kwamitin Gyaran Haraji da Dokokin Kudi na Shugaban Kasa, Taiwo Oyedele da Shugaban Hukumar Rabon Kudaden Gwamnati (RMAFC), Dr. Mohammed Bello Shehu.
Ana shirin amincewa da kudirin haraji
Kwamitin rikon kwarya kan gyaran haraji, wanda Sanata Abba Moro ke jagoranta, an kafa shi a watan Disambar 2024 domin tattauna batutuwan da suka shafi sabbin dokokin haraji tare da Gwamnatin Tarayya.
Sanata Moro ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai yayin tattaunawar bayan samun korafe-korafe daga wasu ɓangarori.
“Mun cimma yarjejeniya bayan tattaunawa mai zurfi da jami’an gwamnati, urinmu shi ne samar da doka wadda za ta dace da bukatun ’yan Najeriya gabaɗaya."
“Lokacin da muka sake haduwa, za mu samu labarin da ya fi kyau."
- Abba Moro.
Ya nuna fatan cewa kwamitin zai kammala aikinsa nan ba da jimawa ba, domin gabatar da dokokin haraji don amincewa.
FIRS ta fadi cigaba da aka samu
Shugaban FIRS, Zacch Adedeji, ya bayyana kwarin gwiwa game da ci gaban da aka samu, ya ce an warware duk wata matsala da ke akwai.
“An tattauna kan wuraren da ake ganin akwai matsala, kuma an samu mafita, ba za mu sake samun wani zama ba, domin duk an warware batutuwa."
“Kowa ya amince cewa Najeriya tana bukatar wadannan dokokin, a yau, mun ga tsarin doka ya haɗa Antoni-janar, ’yan majalisa, da sauran masu ruwa da tsaki."
- Zacch Adedeji.
Adedeji tabbatar da cewa akwai hadin kai tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki kan muhimmancin sababbin dokokin harajin, cewar The Nation.
Kotu ta ba ministoci 2 umarni kan haraji
Kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta umarci Ministan Gida da na shari'a su bayyana gabanta cikin kwanaki uku kan tsarin haraji ga yan kasashen waje.
Kungiyar New Kosol Welfare Initiative ta nemi dakatar da sabon tsarin haraji na (EEL) don kare tattalin arzikin kasa da samar da kuɗin shiga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng