Gwamnatin Tinubu Ta Yi Wa Ma'aikatan da Suka Yi Ritaya Babban Gata

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Wa Ma'aikatan da Suka Yi Ritaya Babban Gata

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara biyan ƙarin kuɗaɗen fansho ga ma'aikatan da suka yi ritaya da ke ƙarƙashin tsarin DBS
  • Ƙungiyar ƴan fansho ta tabbatar da cewa an fara biyan ƙarin na kaso 20% cikin 100% ga ma'aikatan da suka ajiye aikinsu
  • Ta yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan fara biyan ƙarin kuɗaɗen da amincewa da sabon mafi ƙarancin kuɗin fansho

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƴan fansho ta Najeriya (NUP) ta tabbatar da biyan ƙarin kaso 20% na kuɗaɗen fansho ga ma'aikatan da suka yi ritaya da ke ƙarƙashin tsarin DBS.

Ƙungiyar ta yabawa Shugaban kasa Bola Tinubu kan ƙarin kuɗaɗen da kuma fito da tsarin mafi ƙarancin kuɗin fansho na N32,000 ga ma'aikatan da suka yi ritaya.

Gwamnatin tarayya ta fara biyan kudaden fansho
Gwamnatin tarayya ta fara biyan karin kudaden fansho Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Godwin Abumisi, ya sanyawa hannu, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Duk da girke jami'an tsaro, rikici kan kujerar sakataren PDP ya dauki sabon salo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta yi ƙarin kuɗin fansho

Ƙarin na kaso 20% cikin 100%, wanda zai fara aiki tun daga watan Janairun 2024, an fara biyansa ga yawancin ƴan fanshon da ke ƙarƙashin tsarin DBS.

Haka zalika, mafi ƙarancin kuɗin fansho na N32,000, wanda aka amince da shi a watan Yuli 2024, ya fara isa asusun mutane da dama.

A cewar NUP, waɗannan matakai sun nuna soyayya da jajircewar shugaba Tinubu wajen tabbatar da cewa ana tallafawa ma'aikatan da suka yi ritaya a ƙasar tare da kare haƙƙoƙinsu.

Shugaban kasa Tinubu ya samu yabo

Ƙungiyar ta kuma yabawa shugaban ƙasan kan aiwatar da muhimman matakai, don rage matsalolin ƙalubalen tattalin arziƙi da ma'aikatan da suka yi ritaya su ke fuskanta.

Haka kuma, NUP ta godewa hukumar kula da tsarin fansho (PTAD) da sabuwar shugabarta ta ƙasa, Tolulope Odunaiya, bisa tabbatar da biyan ƙarin kuɗin fanshon akan lokaci.

“Wannan ne karon farko da masu fansho za su samu ƙarin kuɗi ba tare da yin zanga-zanga ba. Muna yaba maka, shugaban ƙasa.”

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno, sun yi barna mai yawa

“Muna godiya bisa alƙawarinta na tabbatar da cewa an biya ƙarin kuɗin fansho na kaso 20% cikin 100% kafin ƙarshen watan Disamba 2024 da kuma tsayawa tsayin daka wajen aiwatar da umarnin Shugaba Tinubu kan walwalar masu ritaya."

- Godwin Abumisi

Ƴan fansho sun yi ƙorafi

Sai dai, ƙungiyar ta nuna damuwa kan wasu matsalolin da ke tattare da tsarin biyan kuɗaɗen.

Ta ce duk da nasarorin da aka samu, ba dukkan ma'aikatan da suka yi ritaya ba ne suka samu haƙƙoƙinsu.

NUP ta yi kira ga hukumar PTAD da ta magance waɗannan matsalolin nan take, tare da neman a sake duba takardun domin gyara duk wani kuskure a tsarin biyan kuɗaɗen.

Ƙungiyar ta bayyana cewa tana da kyakkyawan fata kan jajircewar gwamnatin Tinubu wajen kula da ma'aikatan da suka yi ritaya.

Gwamnan Kogi ya ba ƴan fansho alawus

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo ya amince da biyan kuɗaɗen alawus na N10,000 duk wata ga masu karɓar fansho.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun samu nasara, sun sheke gawurtaccen shugaban 'yan bindiga

Gwamna Ododo ya kuma fito da tsarin sanya ƴan fanshon da ke karɓar ƙasa da N50,000 a inshorar lafiya a matakin jiha da ƙananan hukumomi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng