Asiri Ya Tonu: Mutanen Gari Sun Yi Tara Tara, Sun Kama Babban Mawaƙi Ɗauke da Kan Mace

Asiri Ya Tonu: Mutanen Gari Sun Yi Tara Tara, Sun Kama Babban Mawaƙi Ɗauke da Kan Mace

  • Mutanen gari sun kama wani mai waƙoƙin yabon addinin kirista ɗauke da kan wata mata da aka gano cewa budurwarsa ce
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar da cafke mawakin duk da dai ba ta yi cikakken bayani ba
  • Wasu shaidu sun ce mutane sun zargi mawakin ne a lokacin da suka gan shi dauke da bakar jaka kuma kudaje na binsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wani mai waƙoƙin yabo na addinin kirista a Najeriya, Oluwatimileyin Ajayi ya shiga hannu ɗauƙe da kokon kan wata mace da aka gano budurwarsa ce.

An ruwaito cewa an kama mawakin yabon ne a kusa da wata coci ranar Lahadin da ta gabata, 12 ga watan Janairu, 2025.

Yan sandan Najeriya.
Yan sanda sun tabbatar da kama wani mai waƙoƙin yabo ɗauke da kan mace a Nasarawa Hoto: @PoliceNG
Asali: Getty Images

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da kamen

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi magana kan kisan manoma 40, ta fadi abin da ya faru

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kakakin ƴan sandan ba ta yi cikakken bayani ba amma ta tabbatar da cewa ba a Abuja aka kama mawakin ba.

Adeh ta ce:

"Domin ƙarin haske kan lamarin, ba a Abuja aka kama wanda kuke magana a kansa ba, a jihar Nasarawa ne. Ya kamata a riƙa tantance labari kafin yaɗawa don jama'a su fahimta.

Yadda labarin kama mawaƙin ya fara bazuwa

Tun farko wani mai suna Alake ya wallafa a shafin X cewa kama mutumin ɗauke da kan mace ya girgiza shi domin bai taɓa tsammanin haka ba a rayuwarsa.

"Na yi matuƙar kaɗuwa da muka kama wani mai ibada ɗauke da kan mutum (budurwarsa) a kusa a da cocinmu lokacin muna tsakiyar bauta.
"Irin waɗannan abubuwan sai dai na karanta a ko na gani kafafen sada zumuna amma yau na gani da ido na," in ji Alake.

Kara karanta wannan

Bom ya tashi a cikin gida mutane na tsaka da barci, an shiga tashin hankali

Mutane sun cafke wanda ake zargi

A cewar wasu shaidu a shafukan sada zumunta, an ga Timileyin dauke da bakar jaka kuma kudaje na biye da shi.

Hakan ya jawo hankalin jama'a, nan take aka tsare shi kuma aka kwace jaƙar, ana dubawa aka ga sabon kan mutum a ciki.

An tattaro cewa, Timileyin, mai waƙoƙon yabo a coci ya tabbatar da cewa ya yi soyayya da budurwar da ake zargin da cire mata kai na tsawon shekara guda.

Sai dai babu wata hujja da ta tabbatar da wannan ikirari da mawakin ya yi, yanzi haka ne dai yana hannun jami'an tsaro.

Yan sanda sun kama limami da jami'an coci

A wani labarin, kun ji cewa dakarun ƴan sanda sun yi ram da wani limamin coci da ma'aikata kan zarginsu da sakaci a iftila'il da ya faru lokacin rabon tallafin abinci.

Kakakin ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce kuskure ne babba a shirya taro mai girma ba tare da sanar da ƴan sanda, ta ce sakaci ya sa aka kama su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262