Fada Ya Barke Tsakanin Ƴan Ta’adda a Zamfara, an Kashe Fitattun Ƴan Bindiga 2
- An kashe wasu fitattun 'yan ta'adda biyu, Idi Mai Randa da Ya’u, yayin rikici tsakanin bangarorin 'yan bindiga a Zamfara
- Majiya ta tabbatar da mutuwar Idi Mai Randa da Ya’u, wadanda aka sani da jagorantar hare-hare masu yawa a yankin Zamfara
- An ce dakarun Operation Fansan Yanma suna ci gaba da kakkabe 'yan bindigar Zamfara, inda aka kashe shugabanninsu da dama
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Wata rigima ta kaure a tsakanin 'yan ta'addan Zamfara, inda aka kashe fitattun 'yan bindiga biyu, Kachalla Idi Mai Randa da Ya’u.
An ce Idi Mai Randa, wanda ya kware a kai hare-hare a garuruwan Zamfara ya gamu da ajalinsa a wani kwanton-bauna da Dogo Gide ya shirya.
Dogo Gide ya kashe Kachallah Idi Mai Randa
Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa wannan kwanton-baunar ya biyo bayan wasu rikice-rikice masu zafi tsakanin bangarorin 'yan ta'addan biyu a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idi Mai Randa ya jagoranci wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin yaran Dogo Gide, wanda ya sa Gide ya dauki alwashin ramawa.
Mutuwar Idi Mai Randa ta biyo bayan kashe wani abokin aikinsa, Ya’u, wanda aka kama a karamar hukumar Tsafe.
An kashe Ya'u, na hannun daman Mai Randa
Ya’u, wanda ya kasance na hannun damar Kachallah Idi Mai Randa, kuma ana zarginsa da hannu a hare-hare masu yawa a yankin.
Duk da cewa Kachallah Idi Mai Randa ya musanta alakarsa da Ya’u kan safarar wasu makamai, amma yanzu an tabbatar da cewa dukkansu sun mutu.
An samu labarin mutuwarsu daga mabuyarsu a safiyar yau, wanda ke nuna karfin farmakin da aka kai musu.
Sojoji sun tsananta hare-hare a Zamfara
Dakarun Operation Fansan Yanma tare da hadin gwiwar bangaren sojojin sama suna ci gaba da samun nasarori wajen ragargazar 'yan bindiga a maboyarsu.
Wannan hadin gwiwa ya kai ga kashe shugabannin 'yan fashi da dama da kuma kwace kayan aiki masu muhimmanci daga gare su.
A yanzu haka, jami’an tsaro na ci gaba da aikin kakkabe sauran mabuyar 'yan fashi a Zamfara, tare da tabbatar da zaman lafiya.
An kashe mutum 2 a fadan 'yan ta'adda
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani dan bindiga mai suna Kachalla Gajere ya kashe jagoran 'yan ta'adda, Kachalla Tsoho Lulu, a wata arangama da suka yi.
Lamarin ya faru ne a kusa da kauyen Kawaye da ke dajin Bagega, karamar hukumar Anka, jihar Zamfara, inda rikici ya barke tsakaninsu.
Rahotanni sun nuna cewa rikici ya samo asali daga dogon takun sako da ke tsakanin Kachalla Tsoho Lulu da Kachalla Gajere.
Majiyar tsaro ta bayyana cewa magoya bayan Kachalla Tsoho Lulu sun fara neman Kachalla Gajere domin daukar fansa kan kisan jagoransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng