"Ku Murkushe Su": Zulum Ya Nemi Agajin Sojoji da Ƴan Ta'adda Suka Kashe Manoma 40

"Ku Murkushe Su": Zulum Ya Nemi Agajin Sojoji da Ƴan Ta'adda Suka Kashe Manoma 40

  • 'Yan ta'adda sun kai hari a garin Dumba, inda suka kashe manoma 40, yayin da wasu suka tsere kuma ake ci gaba da nemansu
  • Gwamnan Borno ya jajanta wa iyalan da abin ya shafa tare da rokon sojoji su murkushe 'yan ta'addan da ke a yankin Dumba
  • Babagana Umara Zulum ya kuma ja kunnen manoma, masunta da ma sauran jama'a da su guji fita daga yankunan da aka killace

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - A ranar Lahadi, 12 ga Janairun 2025, wasu 'yan ta'adda da ake zargin Boko Haram/ISWAP ne suka kai hari a garin Dumba kusa da yankin Baga.

Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan ta'addan sun kashe mutum 40, yayin da wasu suka tsere kuma ake ci gaba da nemansu har yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi magana kan kisan manoma 40, ta fadi abin da ya faru

Zulum ya yi magana yayin da 'yan ta'adda suka kashe manoma 40 a Dumba
Gwamnan Borno ya nemi sojoji su murkushe 'yan ta'addan da suka kashe manoma 40. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

An fara bincike kan yadda wannan harin ya faru, kamar yadda Zagazola Makama, masani kan tsaro, ya bayyana a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Zulum ya roki sojoji su murkushe 'yan ta'adda

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna tsananin takaici tare da yin Allah-wadai da wannan hari.

Ya yi kira ga sojojin Operation Hadin Kai da su gano tare da kawar da 'yan ta'addan da ke gudanar ayyukan ta'addanci a yankin Dumba.

Gwamnan ya kuma jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da iyalansu, yana mai ba da tabbacin cewa za a nemo wadanda suka ɓace.

Zulum ya jajantawa iyalan wadanda aka kashe

Gwamna Zulum ya ce:

"Cikin bakin ciki da jimami, na samu labarin wannan mummunan hari da aka kai kan manoma da masu kamun kifi a Dumba.
"A madadin gwamnatinmu, muna mika sakon ta'aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa. Za mu yi duk mai yiwuwa don ganin an dauki mataki."

Kara karanta wannan

Bello Turji ya farmaki masallaci a Zamfara, ya yi garkuwa da masu ibada

Gwamna Zulum ya kuma yi kira ga dakarun tsaro da su ci gaba da aikin kashe 'yan ta'adda a yankunan tafkin Chadi da ma sauran wurare.

Manoma sun fita daga yankunan da aka killace

An lura cewa manoman sun fita daga yankin da ake da tsaro zuwa wani wuri da har yanzu ba a kammala tsaftace shi daga abubuwan fashewa ba.

Irin waɗannan wuraren suna da hatsarin gaske musamman hare-hare daga 'yan ta'adda da kuma tashin nakiyoyin da aka dasa a kasa.

Zulum ya gargadi jama'a da su guji fita daga yankunan da aka yi wa alama don kare lafiya da kuma rayuwarsu.

Zulum ya gargadi manoma da masuntan Borno

Gwamnan ya ce an ware filayen da za a iya gudanar da aikin noma, yayin da sojoji ke ci gaba da tsaftace yankunan da ke da haɗari.

"Ya zama wajibi jama'armu su tsaya cikin wuraren da ke da tsaro, inda za su samu damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali,"

Kara karanta wannan

Harin sojoji: Gwamna ya jajanta, ya yaba wa jami'an tsaro kan tarwatsa yan bindiga

- Inji Zulum.

Gwamnatin Borno ta yaba wa sojoji kan ƙoƙarinsu na tsaftace manyan yankuna don maido da al'umma zuwa gidajensu da dawo da ayyukan noma a jihar.

Fashewar bam ya kashe manoman Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa an kashe akalla mutum uku sakamakon fashewar tagwayen bam a karamar hukumar Damboa, jihar Borno.

Bama-baman sun tashi ne bisa kuskure yayin da sojoji ke aikin kakkabe mabuyar 'yan ta'adda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.