Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Hanyar Warware Rikicin Kudirin Haraji ga Gwamnoni

Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Hanyar Warware Rikicin Kudirin Haraji ga Gwamnoni

  • Mai ba wa shugaban kasa shawara kan sadarwa, ya ce gwamnonin da suke da matsala da kudirin gyaran haraji su tunkari majalisar kasa
  • Daniel Bwala ya ce gwamnonin da suke wa’adi na biyu ne suka fi sukar kudirin, yayin da masu wa’adi na farko basu nuna damuwa sosai ba
  • Hakan na zuwa ne yayin da wasu shugabannin Arewa suka zargi kudirin da fifita jihar Legas da kuma cutar da yankin Arewacin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mai ba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan sadarwa, Daniel Bwala ya yi kira ga gwamnonin da suke adawa da kudirin haraji su maida hankalinsu ga majalisar kasa.

A wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin, Bwala ya bayyana cewa ba wai duka gwamnonin ne ke adawa da kudirin ba.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya ragargaji Bola Tinubu kan hauhawar farashi

Bwala
Gwamnatin Tinubu ta bukaci a daina surutu kan kudirin haraji, Hoto: Bayo Onanuga|Daniel Bwala
Asali: Twitter

The Nation ta wallafa cewa Bwala ya yi magana ne a kokarinsa na wayar da kai game da kudirin haraji da ya haifar da muhawara mai zafi a fadin kasa, musamman daga wasu bangarorin Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adawar 'yan Arewa ga kudirin haraji

Tun lokacin da aka mika kudirin gyaran haraji ga majalisar kasa a ranar 3 ga Oktoba, 2024, lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin gwamnonin Arewa.

Kungiyar gwamnonin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya na Arewa sun yi watsi da kudirin, suna masu kira da cewa zai cutar da yankinsu.

Sun yi ikirarin cewa kudirin zai fifita jihar Legas da wasu jihohi ‘yan kadan, suna kuma ganin zai rage kudin shiga na da yawan jihohi.

Sai dai Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Bwala ya ce;

“Yawancin gwamnonin Arewa ne suka fi magana kan kudirin, amma gaskiya ita ce, kudirin zai shafi dukkan jihohin da kudin shigarsu zai ragu idan aka yi amfani da tsarin."

Kara karanta wannan

Magana ta dawo sabuwa, kotu ta ba Ministocin Tinubu 2 umarni kan kudirin haraji

Ya kara da cewa, kamata ya yi gwamnonin su daina kallon lamarin a matsayin Arewa da Kudu, domin kudirin na da alaka da ci gaban kasa baki daya.

Amfanin kudirin ga jama’ar Najeriya

A cewar Bwala, kudirin zai amfanar da daukacin ’yan Najeriya sama da miliyan 200, fiye da gwamnonin da suke jihohi 36 da birnin tarayya Abuja.

Bwala ya ce,

“Idan har burinmu shi ne ci gaban ’yan Najeriya, kamata ya yi mu maida hankali kan dimbin mutanen da za su amfana da tsarin,
"Ba wai mu tsaya kan adawar wasu gwamnonin da za su ji ciwon ragin kudin shiga ba.”

Ya kuma bayyana cewa sauye-sauyen da aka yi a kudirin suna da nufin bunkasa tattalin arziki da habaka haraji a fadin kasar.

Yadda za a shawo kan matsalolin haraji

Bwala ya bukaci gwamnonin da suke da matsala da kudirin su tunkari wakilan jihohinsu a majalisa domin tattauna matsalolinsu.

Kara karanta wannan

"Ba talaka ba ne a gabansu," Hadimin Tinubu ya faɗi dalilin gwamnoni na sukar ƙudirin haraji

“Idan gwamnonin suna da wata matsala da kudirin kamata ya yi su tunkari ’yan majalisunsu daga jihohinsu domin warware matsalar,
Ba wai su rika yin maganganu a bainar jama’a ba.”

Ya kuma yi kira ga majalisar dokoki da ta tabbatar da cewa duk wata matsala da aka kawo za a duba ta cikin adalci da gaskiya, domin tabbatar da cewa kudirin sun amfanar da Najeriya.

Hadimin Buhari ya shawarci Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa mai ba tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan noma ya ce ba a ba Bola Tinubu shawara mai kyau kan rage farashin abinci ba.

Legit ta wallafa cewa hadimin tsohon shugaban kasar ya ce tsadar sufuri da cire tallafin mai na cikin dalilan da suka sanya tsadar abinci a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng