'Yan Kabilar Ibo Sun Goyi Bayan Sake Zaben Tinubu, Sun Mika Bukatarsu ga Gwamnati

'Yan Kabilar Ibo Sun Goyi Bayan Sake Zaben Tinubu, Sun Mika Bukatarsu ga Gwamnati

  • Kungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu domin ya zarce a mulkin kasar nan
  • Sai dai bayan nuna goyon bayanta, kungiyar ta mika muhimmiyar bukata ga gwamnatin tarayya a kan lamarin Nnamdi Kanu
  • Ohanaeze ta roƙi shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon mulkinsa domin sakin jagoran IPOB, a cikin wannan shekarar ta 2025

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Enugu - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu cikakken goyon baya daga ƙungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo domin sake zabarsa a kakar zaɓen 2027 mai zuwa.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, 12 Janairu, 2025, mai ɗauke da sa hannun mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mazi Okechukwu Isiguzoro, kungiyar ta mika bukata ga gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

"Za a haura N70,000": Gwamnatin Tinubu za ta ƙara mafi ƙarancin albashi a Najeriya

Tinubu
Kungiyar kabilar Ibo ta goyi bayan Tinubu ya zarce a mulkin Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Ohanaeze Ndigbo, babbar ƙungiyar al’adu da zamantakewar kabilar Ibo, ta roƙi Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon mulkinsa don tabbatar da sakin Kanu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibo sun fadi muhimmancin sakin Nnamadi Kanu

Legit ta wallafa cewa kungiyar Ohanaeze ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya tabbatar da cewa gwamnati ta saki shugaban 'yan kungiyar aware ta IPOB, Nnamdi Kanu a shekarar 2025.

A cewar Mazi Isiguzoro, sakin Kanu zai zama muhimmin mataki wajen dawo da zaman lafiya da kuma magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin Kudu maso Gabas.

Ya ce:

“Dole ne yankin kudu maso gabas ya samu hanyar zaman lafiya mai dorewa, domin ba za a iya cimma kwanciyar hankali a cikin yanayin tashin hankali da rikici ba.”

Kungiyar kabilar Ibo ta musanta hadaka

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta musanta rade-radin da ake yi na haɗakar jam’iyyu masu adawa da gwamnatin Tinubu, tana mai cewa bai kamata a ɓata lokaci a kan hakan ba.

Kara karanta wannan

Yarjejeniyar $2bn: Shugaba Tinubu ya roki arziki da ya hadu da Ministan China

Sanarwar ta bayyana cewa:

“Goyon bayan Ohanaeze Ndigbo ga Shugaba Tinubu a 2027 wata manufa ce mai ƙarfi wacce ke nuna jajircewarmu ga zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaban ababen more rayuwa a kudu maso gabas.”

'Yan kabilar Ibo sun nemi a hada kai

Kungiyar ta kuma yi kira ga membobinta da duk al’ummar Ibo da su haɗa kai domin tabbatar da ci gaba da samun nasarori ga yankinsu.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

“Mun kira dukkan membobinmu da al’ummar Ibo gaba ɗaya da su jingina da wannan hangen nesa, su ajiye son zuciya, su mai da hankali kan wata manufa guda wacce za ta kawo ci gaba na gaskiya ga yankinmu.”

Ohanaeze Ndigbo ta ƙara jaddada cewa sun sadaukar da kansu ne ga ci gaban yankin domin habaka tattalin arziki da rayuwar mazauna yankin Ibo.

'Yan kabilar Ibo sun soki Atiku

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo ta nuna rashin jin daɗinta kan kalaman tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, game da goyon bayansa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

A wata sanarwa da Sakatare-Janar na tsagin kungiyar, Okechukwu Isiguzoro, ya fitar, kungiyar ta bayyana cewa kalaman Atiku sun kara tsananta matsalar siyasa tsakanin yankin Arewa da Kudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.