Hajj 2025: NAHCON Ta Fadi Sunayen Kamfanonin Jirage 4 da Za Su Yi Jigilar Alhazai

Hajj 2025: NAHCON Ta Fadi Sunayen Kamfanonin Jirage 4 da Za Su Yi Jigilar Alhazai

  • Fadar shugaban kasa ta zabi kamfanonin jirage huɗu da za su yi jigilar alhazai, ciki har da Air Peace, Fly-Nas, Max Air da UMZA
  • An gudanar da tantance kamfanoni 11 bayan an kafa kwamitin tantancewa mai mambobi 32 daga hukumomi daban-daban
  • Hukumar NAHCOM ta sanar da cewa ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Hajjin 2025 tsakanin Najeriya da Saudiyya a Jiddah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fadar shugaban kasa ta amince da kamfanonin jirage huɗu da za su yi jigilar alhazai a Hajjin 2025, yayin da NAHCON ta cimma yarjejeniya da Saudiyya.

Fatima Sanda Usara, mataimakiyar daraktar yada labarai ta NAHCON, ta bayyana hakan a sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, 12 ga Janairu.

NAHCON ta yi magana yayin da ta zabi jiragen da za su yi jigilar alhazan bana
Shirin aikin Hajjin bana: NAHCON ta zabi kamfanonin jirage 4 da za su yi jigilar alhazai. Hoto: @MaxAirLtd
Asali: Facebook

An zabi jiragen da za su yi jigilar alhazai

Usara ta fitar da sanarwar ne a madadin shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ta kuma wallafa a shafin X na hukumar.

Kara karanta wannan

Ya na ji ya na gani: Dalilai 5 da za su iya hana gwamnan APGA samun tazarce a 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NAHCON ta bayyana cewa kamfanonin jiragen da aka zaba sun fito daga cikin kamfanoni 11 da suka nemi aikin jigilar alhazan Najeriya a bana.

Kamfanonin da aka zaba sun haɗa da Air Peace Limited, Fly-Nas, Max Air da UMZA Aviation Services Limited.

Yadda aka kafa kwamitin tantance jiragen

Wani kwamitin tantancewa mai mambobi 32 da shugaban NAHCON ya kafa ranar 26 ga Nuwamba 2024 ne ya gudanar da tantance kamfanonin.

'Yan kwamitin sun haɗa da wakilai daga hukumar jin daɗin alhazai ta jihohi, da mambobi uku daga hukumar kula da jiragen sama ta kasa (NCAA).

Sauran sun haɗa da wakili daga hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa (FAAN), da hukumar gudanar da sararin samaniya ta kasa (NAMA).

Haka nan, akwai wakili daga hukumar hasashen yanayi ta kasa (NIMET) da hukumar binciken lafiyar jiragen sama (NSIB).

An kuma samu wakili daga hukumar kwastam ta kasa (NCS) da hukumar yaki da cin hanci (ICPC).

Kara karanta wannan

Wani shugaban karamar hukuma ya sake nada hadimai 130 watanni 6 da nadin mutum 100

Sauran wakilan sun haɗa da mambobin NAHCON daga kowace shiyya ta ƙasa, da shugabannin NAHCON daga sassan sufurin jiragen sama, shari’a, binciken kudi, da sauransu.

An zabi jiragen jigilar kayan alhazai

Haka nan, an zabi kamfanoni uku da za su yi jigilar kayan alhaza da suka wuce ƙima a hajjin bana.

Kamfanonin sun haɗa da Aglow Aviation Support Services Limited, Cargozeal Technology Limited, da Qualla Investment Limited.

Shugaban NAHCON ya taya kamfanonin da suka yi nasara murna, tare da jaddada musu muhimmancin cika alkawuran da suka ɗauka yayin tantancewa.

NAHCON ta cimma yarjejeniyar Hajji da Saudiyya

A wani cigaba, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin hajjin 2025 da ma’aikatar Hajj da Umrah ta Saudiyya.

Taron ya gudana ne ranar 12 ga Janairu 2025 a birnin Jeddah na Saudiyya don tabbatar da shirye-shiryen hajjin bana.

A tawagar shugaban NAHCON akwai shugaban kwamitin harkokin ketare na majalisar dattawa, Sanata Abubakar Sani Bello.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi alakarsa da El-Rufai, ya magantu kan barinsa APC da hana shi Minista

Haka nan akwai shugaban kwamitin alhazai na majalisar wakilai, Hon. Jafaru Muhammed Ali.

Sauran sun haɗa da wakilin Najeriya a Riyadh, Dr Ibrahim Modibbo; Jakadan Najeriya a Jeddah, Ambasada Mu’azzam Nayaya; da Ambasada Mahmud Lele.

Gwamna ya fara karbar kudin aikin Hajji

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Bauchi ta amince da fara karɓar Naira Miliyan 6.5 daga hannun maniyyatan Hajjin 2025 a matsayin kudin kafin alkalami.

An fara karɓar kudin kafin alkalamin ne ranar Laraba, 11 ga Satumba, 2024, kafin a kayyade cikakken kudin aikin hajjin na shekarar 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.