Hadimin Buhari Ya Ragargaji Bola Tinubu kan Hauhawar Farashi
- Tsohon mai bai wa Buhari shawara, Dolapo Bright ya ce an yaudari Bola Tinubu cewa janye harajin shigo da kayan abinci zai rage hauhawar farashi
- Dolapo Bright ya ce hauhawar farashin man fetur da dizil da ake amfani da su wajen sufuri na da muhimmanci wajen ƙara tsadar kayan masarufi
- Bright ya ce gwamnatin Tinubu na taka rawa wajen haifar da tsadar kayayyaki saboda tsare-tsaren tattalin arzikinta da ke kawo cikas ga manoma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mai bai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin noma ya ce an bai wa Bola Tinubu shawara marar kyau kan sauke farashi.
Dolapo Bright ya ce an ba Tinubu shawarar cewa janye haraji da kudi kan kayan abinci da ake shigowa da su zai rage farashin kaya, wanda ba haka ba gaskiya ba ne a cewarsa.
Bright ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a wani shiri na musamman da aka gabatar a tashar Channels Television ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsadar sufuri da tsare tsaren Bola Tinubu
Bright ya bayyana cewa matakin janye haraji kan kayan abinci ba zai yi tasiri ba saboda tsadar sufuri da sauran matsalolin tattalin arziki.
“Wanda ya ba da wannan shawara bai fahimci abin da ke faruwa a Najeriya ba. Idan za ka shigo da kaya daga waje, za su iso ne ta Legas, kuma dole ne a kai su zuwa jihohi daban-daban.
"Wannan yana nufin karin tsada, wanda ba zai taimaka wa noma a cikin gida ba.”
- Dolapo Bright
Daily Post ta wallafa cewa Bright ya ce wannan matakin zai hana noma ci gaba saboda za a fi mayar da hankali kan kayan da ake shigo da su daga waje.
Tasirin hauhawar farashi a Najeriya
Tun bayan rantsar da shugaba Bola Tinubu a watan Mayun 2023, hauhawar farashi a Najeriya ta ƙaru sosai.
A cewar Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), adadin hauhawar farashi ya kai 22.41% a lokacin da aka rantsar da Tinubu, amma ya ƙaru zuwa 34.6% a watan Nuwamban 2024.
Har ila yau, hauhawar farashin kayan abinci ta kai 39.93% daga 32.84% a shekarar da ta gabata, inda kayan abinci kamar su shinkafa, kifi, fulawa, hatsi, da kaza suka fi tsada.
Rashin tallafi ga manoma da tsadar kaya
Bright ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan masarufi na da alaƙa da tsadar man fetur da disil da ake amfani da su wajen noma da sufuri.
“Yawancin manoma ba su iya samar da kaya kamar yadda suka saba saboda tsadar kayan aiki da na'urori.
"Idan gwamnati ta samar da yanayi mai kyau, manoma za su iya aiki ba tare da dogaro da ita ba.”
- Dolapo Bright
'Za mu kwace mulki daga hannun Tinubu' - PDP
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ce ta shirya tsaf domin tunkarar shugaba Bola Tinubu da jam'iyyarsa ta APC a 2027.
Jam'iyyar PDP ta ce zaben 2027 zai bude sabon babi a tarihinta inda ta ke shirin dawowa da karfinta wajen sake rike ragamar siyasar Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng