Salon 'Yan Ta'adda na Tura Kudi wa Mutane domin Garkuwa da Su ta Yanar Gizo
- Rundunar ‘yan sandan Lagos ta gano sabon salon garkuwa da mutane, inda ake yaudarar mata ta hanyar yin soyayya da su ta yanar gizo
- 'Yan sanda sun ceto mata 16 da aka yaudara ta wannan hanyar, inda aka gano suna fuskantar barazana daga masu garkuwa da su
- Kwamishinan ‘Yan Sanda na Lagos, CP Olawale Ishola, ya gargadi al’umma musamman mata da su guji amincewa da baki a yanar gizo
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta bayyana sabon salon garkuwa da mutane inda masu aikata laifin ke yaudarar mata ta hanyar yin soyayya da su a kafafen sada zumunta.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Olawale Ishola, ya sanar da cewa rundunar ta ceto mata 16 da suka fada tarkon wannan dabara daga watan Satumban 2024 zuwa Janairun 2025.
Vanguard ta wallafa cewa CP Ishola ya ce masu garkuwa da mutanen suna amfani da dabaru wajen yaudarar matasa mata domin su fada tarkon su ba tare da sun sani ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabuwar dabarar masu garkuwa da mutane
CP Ishola ya bayyana cewa masu garkuwa suna amfani da kafafen sada zumunta wajen haduwa da matan suke son sacewa.
Kwamishinan 'yan sandan ya ce;
“Masu garkuwa suna fara da neman abota a kafafen sada zumunta, suna amfani da soyayya da alkawura masu gwabi domin su ja hankali.
"Suna tura musu tikitin jirgi da ya kai har N500,000, da kuma da kama musu masauki a manyan otal.”
A lokacin da matan suka isa Lagos, miyagun na kwace wayoyinsu, sannan a tura kudinsu zuwa asusun masu garkuwan.
Daga nan, masu garkuwan suna kira iyalan waɗanda suka yaudara domin neman kuɗin fansa, tare da yi musu barazana.
'Yan sanda sun ceto mata 16 a Lagos
Kwamishinan ya bayyana cewa an samu nasarar ceto mata 16 da aka kama ta hanyar dabarar, kuma rundunar ta ci gaba da yin aiki tuƙuru domin ganin an rage aikata laifin.
CP Ishola ya ce;
“Wannan dabara ta zama matsala domin mata suna barin jihohinsu su tafi Lagos domin haduwa da abokan da ba su sani ba. A lokacin da suka isa, sai a mayar da su kamar bayi.”
Kwamishinan ya gargadi jama’a, musamman mata, da su kula da yadda suke hulɗa da mutane a kafafen sada zumunta.
CP Ishola ya ce duk wanda ya ga wani motsin da bai yarda da shi ba ya sanar da hukuma domin su ɗauki matakin da ya dace.
An kama budurwar da ta yaudari iyayenta
CP Ishola ya bayar da labarin wata budurwa ‘yar shekara 14 wacce ta ce an yi garkuwa da ita, amma daga baya aka gano tana tare da saurayinta ne.
Rundunar 'yan sanda ta ce a ranar 8 ga Janairu, 2025, iyayenta suka kai rahoton ɓatarta, daga baya, masu garkuwan suka turo asusun da za a biya kuɗin fansa.
Bayan bincike, rundunar ta gano cewa budurwar tana tare da saurayinta ne da suka kitsa karyar an sace ta.
An kama masu garkuwa a jihohi
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta kama masu garkuwa da mutane a jihohi da dama yayin wani artabu da suka yi.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an 'yan sanda sun kai farmaki ne a jihohin Nasarawa, Benue da Bayelsa kuma sun kwato tarin makamai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng