Gwamnatin Bauchi Ta Soki Martanin Hadimin Tinubu kan Batun Kudirin Haraji

Gwamnatin Bauchi Ta Soki Martanin Hadimin Tinubu kan Batun Kudirin Haraji

  • Gwamnatin Bala Mohammed ta caccaki kalaman Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Yada Labarai, Sunday Dare
  • Mukhtar Gidado, mai ba gwamnan Bauchi shawara a kan yaɗa labarai ya bayyana kalaman Dare a matsayin na rashin kwarewa
  • Gwamnatin Bauchi ta jaddada cewa gwamnan ya yi magana bisa kishin ƙasa, tare da neman gyaran dokokin haraji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta ta soki kalaman da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Yada Labarai da Sadarwa, Mista Sunday Dare, ya yi kan Gwamna Bala Mohammed. Gwamnatin ta ce Mista Dare ya nuna tsantsar rashin ƙwarewa da rashin kishin ƙasa, duba da lokacin da ya yi martanin ana tunawa da sojojin Najeriya da suka kwanta dama.

Kara karanta wannan

Cire tallafin fetur ya fara haifar da sauƙi ga talakawa, cewar hadimin Tinubu

Bauchi
Gwamnatin Bauchi ta sake sukar gwamnatin Tinubu Hoto: Senator Bala AbdulKadir Mohammed/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Gwamna Bala Mohammed ya bayyana rashin gamsuwarsa kan dokokin gyaran haraji da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar ga majalisa. Kakkausan sukar gwamnan ce ta sa Dare ya mayar da martanin da bai yi wa gwamnatin Bauchi dadi ba, aka bayyana hadimin Tinubu a matsayin wanda bai san aiki ba.

Gwamnatin Bauchi ta caccaki hadimin Tinubu

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa gwamnatin Bauchi ta bayyana martanin Dare a matsayin wanda bai dace da matsayin mai magana da yawun shugaban ƙasa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Bauchi ta fusata kan martanin hadimin shugaban kasa a wata sanarwa da Mai Bai wa Gwamna Bala Mohammed Shawara Kan Yada Labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar.

An zargi gwamnatin Tinubu da rashin girmama ƙasa

Gwamnatin jihar Bauchi ta caccaki hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu inda ta ke ganin bai dace da muƙamin mai magana da yawun shugaban ƙasa ba.

Sanarwar da Mukhtar Gidado ya fitar ta ƙara da cewa ;

Kara karanta wannan

Yarjejeniyar $2bn: Shugaba Tinubu ya roki arziki da ya hadu da Ministan China

“Maganganun Mista Dare ba su dace da matsayin da ya kamata a nuna a matsayin mai magana da yawun shugaban ƙasa ba.
Kalaman sun yi muni musamman da aka yi su a lokacin da ake gudanar da sallar Juma’a da kuma tunawa da Ranar Sojojin da suka sadaukar da rayukansu. Wannan lamari ya nuna rashin girmama al’amuran ƙasa masu muhimmanci.”

Gwamnatin Bauchi ta shawarci hadimin Tinubu

Mukhtar Gidado ya bayyana cewa, ya kamata wanda ke wakiltar shugaban ƙasa ya kasance mai girmama mutunci da yanayin zaman lafiya. Ya ce irin wannan halayya ta Dare, wadda ke cike da sukar lamuran siyasa fiye da bauta wa ƙasa, bai dace da ofishinsa ba. Gidado ya kara da cewa;

“Maimakon mayar da hankali kan jawaban kishin ƙasa, Mista Dare ya koma amfani da maganganun ɓangaranci da kaucewa batutuwan da suka fi muhimmanci.
Wannan ba shi ne abin da ake tsammani daga mai wakiltar shugaban ƙasa ba.”

Kara karanta wannan

Gwamna ya gama sukar Tinubu, zai kashe N400m don sayen kwamfuta 6

Gwamnatin Bauchi ta soki Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala AbdulKadir Mohammed, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan salon mulkin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce dokar gyaran haraji da Tinubu ya bijiro da shi ta na iya jefa jihohi, musamman na Arewa, cikin ƙarin matsaloli da mawuyacin hali, kuma ya kin shawara a kan batun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.