Turji Ya Farmaki Masallaci a Zamfara, Ya Yi Garkuwa da Masu Ibada

Turji Ya Farmaki Masallaci a Zamfara, Ya Yi Garkuwa da Masu Ibada

  • Shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji da mabiyansa sun farmaki masallacin Birnin Yaro, Jihar Zamfara yayin da ake tsaka da sallah
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Turji ya sace adadi mai yawa na masu ibada, inda ya mika su cikin daji domin garkuwa da su
  • Ana zaton Turji ya kai harin ne saboda rugugin wuta da ga ke sha daga Sojojin Operation fansan yamma a kokarin kawo karshensa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Jama'a sun shiga fargaba bayan 'yan bindiga karkashin jagorancin fitaccen shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji, sun kai wani mummunan Zamfara.

Fitinannun 'yan bindiga ɗauke da mugayen makamai sun kai hari wani masallaci da ke kauyen Birnin Yaro da ke jihar Zamfara a lokacin da jama'a ke sallah.

Kara karanta wannan

Harin sojoji: Gwamna ya jajanta, ya yaba wa jami'an tsaro kan tarwatsa yan bindiga

Turji
Turji ya sace masallata a Zamfara Hoto: Kamal Muhammad
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa maharan sun mamaye masallacin yayin sallar Isha a daren Juma’a, inda suka farmaki bayin Allah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Turji da ‘yan bindigar sa sun kutsa cikin masallacin, inda suka tayar da hankalin al’umma masu ibada da na kewaye yayin da su ka rika tayar da hatsaniya.

Turji ya yi garkuwa da mazauna Zamfara

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji ya yi garkuwa da adadi mai yawa na masu ibada da ya sace daga masallaci a Zamfara.

Kawo lokacin hada wannan rahoton, ba a tantance adadin mutanen da aka sace ba a harin da ya tayar da hankulan mazauna kauyen Birnin Yaro. An ruwaito cewa maharan sun ingiza wadanda aka kama zuwa cikin daji, yayin da su ka bar sauran mutanen da ba a kwashe ba a cikin zulumi.

Turji: An yi hasashen dalilin garkuwa da jama'a

Rahotanni sun nuna cewa Bello Turji na iya amfani da mutanen da ya kama a matsayin garkuwa don kare kansa daga hare-haren sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bello Turji na tsaka mai wuya, sojojin Najeriya sun yi wa yaransa ruwan wuta a Zamfara

A halin yanzu, dakarun sojoji karkashin atisayen Operation FANSAN YANMMA su na kai zafafan farmaki a kan Turji da mabiyansa da suka addabi jama'ar Zamfara da kewaye.

Wannan aman wuta da 'yan ta'addan ke fuskanta ya biyo bayan umarnin Shugaban kasa, Bola Tinubu na a kawo karshen Turji da ta'addanci a cikin gaggawa.

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Christopher Musa ya umarci sojojin da su tabbata an kawo karshen Bello Turji, yayin da ɗan ta'addan ya yi barazana ga mazauna Zamfara.

Bello Turji ya shiga matsala

A baya, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara a kokarinta na kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankin Arewa maso Yamma.

Zaratan dakarun sun bude wuta a jihar Zamfara, inda ake cigaba da yin luguden wuta kan mabiyan kasurgumin ɗan ta'adda, Bello Turji, lamarin da ya sa su neman tsira.

Mai magana da yawun rundunar sojin sama, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya bayyana cewa rundunar ta samu nasarar kashe 'yan bindiga da dama a wannan harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.