"Har Yanzu Babu Hujja," Rundunar Soji Ta Yi Magana kan Kuskuren Jefa Bom a Zamfara

"Har Yanzu Babu Hujja," Rundunar Soji Ta Yi Magana kan Kuskuren Jefa Bom a Zamfara

  • Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce babu wata hujja da ke nuna jirgin yaƙi ya yi kuskuren kashe ƴan banga da fararen hula a Zamfara
  • Rahoto ya nuna cewa wani jirgin sojoji ya jefawa mutane bom a kauyen Tungar Kara da ke yankin Maradun, ana fargabar kashe jami'an tsaro da fararen hula
  • Mai magana da yawun rundunar sojin sama watau NAF, Olusola Akinboyewa, ya ce rahoton ba gaskiya ba ne domin babu wata hujja

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta musanta rahotannin da ake yaɗawa cewa jirgin yaƙi ya yi kuskuren kashe bayin Allah a jihar Zamfara.

Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa jirgin ya sakar wa waɗanda ba ruwansu bom, ya kashe akalla mutum 16 a kauyen Tungar Kara, yankin Maradun.

Kara karanta wannan

Harin sojoji: Gwamna ya jajanta, ya yaba wa jami'an tsaro kan tarwatsa yan bindiga

Taswirar Zamfara.
Rundunar sojin sama ta musanta rahoton da ake cewa ta kashe waɗanda ba ruwansu a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ana fargabar sojoji sun kashe fararen hula

Wani rahoto daga Zagazola Makama, mai sharhi kan al'amuran tsaro a yankin Tafkin Chadi, ya ambato cewa wadanda suka mutu sun hada da askarawa da wasu mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana fargabar jirgin sojojin ya kashe dakarun kariya na Zamfara (ZCPG) waɗanda aka fi sani da askarawa, ƴan banga da wasu da ake zargin suna da alaka da ƴan bindiga.

Rundunar sojojin sama ta yi magana

Sai dai a wata hira da The Cable, daraktan hulda da jama'a na NAF, Olusola Akinboyewa, ya karyata wadannan zarge-zargen na kisan waɗanda ba ruwansu.

A rahoton Daily Trust, kakakin NAF ya ce:

"Rundunar sojin sama tana amfani da duk wata hanya don kaucewa ko rage asarar rayukan fararen hula yayin gudanar da ayyukanta.
"Wadannan rahotanni na iya fitowa daga 'yan ta'adda da magoya bayansu a matsayin hanyar bata sunan sojoji da farfaganda, ganin cewa yanzu an matsa masu lamba."

Kara karanta wannan

Bello Turji na tsaka mai wuya, sojojin Najeriya sun yi wa yaransa ruwan wuta a Zamfara

Sojoji sun ce babu hujjar kashe mutane a Zamfara

Akinboyewa ya kara da cewa babu wani sahihin rahoto da ke nuna an samu asarar rayukan fararen hula, kuma hare-haren sun kasance bisa sahihan bayanai.

"Duk da haka, muna ƙara tabbatar da cewa rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ba ta kai samame kan 'yan bindiga, 'yan ta'adda da sauransu sai ta gama haɗa bayanan sirri masu tushe.
"Bangaren sojin sama na Operation Fansan Yamma ne ya kai hare-haren da ake surutu a kai da nufin magance hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa kauyuka a yankin.
"A halin yanzu, ba mu samu wani sahihin rahoto da ke cewa an yi asarar rayukan fararen hula a wannan farmaki ba, idan mun samu bayani zamu sanar da al'umma."

- In ji mai magana da yawun NAF, Akinboyewa.

Sojoji sun far wa sansanin Bello Turji a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa gwarazan sojoji sun kai samame ta sama kan sansanin ƴan bindiga masu alaka da ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji.

Hukumar sojojin sama ta ce samamen ya yi nasara an kashe manya da kananan mayakan Bello Turji, sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262