Harin Sojoji: Gwamna Ya Jajanta, Ya Yaba wa Jami'an Tsaro kan Tarwatsa Yan Bindiga

Harin Sojoji: Gwamna Ya Jajanta, Ya Yaba wa Jami'an Tsaro kan Tarwatsa Yan Bindiga

  • Gwamna Dauda Lawal ya yaba wa kokarin sojojin Najeriya a sabon farmakin da suka kai kan 'yan bindiga a Jihar Zamfara.
  • Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya ta kai harin jirgin sama kan 'yan bindiga da ke kai farmaki a Zurmi da Maradun.
  • Gwamnatin Zamfara ta jajanta wa iyalan jami'an JTF da aka rasa a Tungar Kara, yana tabbatar da goyon baya ga tsaro da wanzar da zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gusau, Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yaba wa kokarin sojoji game da farmaki kan yan bindiga.

Gwamnan ya kuma jajanta wa iyalan wadanda suka gamu da tsautsayi na harin sojoji a jihar inda ya yi wa iyalansu albashir.

Gwamna ya yaba wa kokarin sojoji a farmaki kan yan bindiga
Gwamna Dauda Lawal ya jajanta wa wadanda suka rasa rayukansu yayin karin sojoji. Hoto: Dauda Lawal Dare.
Asali: Facebook

Dauda Lawal ya yi ta'azziya kan harin bam

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Sulaiman Bala Idris ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Bello Turji na tsaka mai wuya, sojojin Najeriya sun yi wa yaransa ruwan wuta a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan fararen hula da harin ya shafa a Tungar Kara, Zurmi.

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kai harin jirgin sama a karshen mako, inda ta yi wa 'yan bindiga da ke kai farmaki a Zurmi da Maradun barna.

Sanarwar ta bayyana cewa fararen hular da abin ya shafa mambobin yan banga ne, da aka yi kuskuren cewa 'yan bindigar da suka tsere.

“Mun samu rahotanni masu game da nasarar hare-haren da 'Operation Fansar Yamma' ta kai a Zurmi da Maradun."
“Harin ya rage karfin 'yan bindigar sosai kuma ya nuna jajircewar rundunar sojojin sama na kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu."
“Gwamnati tana tabbatar da cewa za ta ci gaba da mara baya ga kokarin tsaro da aka samu don wanzar da zaman lafiya."

- Cewar sanarwar

Dauda Lawal ya yi albashir ga sojoji

Gwamnatin ta sake tabbatar da goyon bayanta ga sojoji don ganin da an kai ga nasara a yakin da ake yi da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Auren jinsi: Tinubu ya kawo sabuwar doka ga sojoji kan luwadi da madigo, ya yi gargadi

“Za mu ci gaba da bayar da tallafi don karfafa bayanan sirri, samar da kayan aiki, da karfafa hadin kai don cimma zaman lafiya."
“Abin takaici, wasu mambobin JTF da 'yan banga sun rasa rayukansu a Tungar Kara, muna addu’a Allah ya gafarta musu ya ba su Aljannah."
“Gwamnati na jajanta wa iyalan wadanda suka rasu kuma za ta ba su dukkan tallafin da ya dace.”

- Sulaiman Bala Idris

Daga karshe, gwamnati ta yi kira ga jama’a da su kasance masu kula da tsaro, su kai rahoton duk wani abu da ake zargi, tare da hadin kai don kawo karshen 'yan bindiga.

Sojoji sun kai hari kan yaran Turji

Kun ji cewa Sojojin sama sun yi luguden wuta kan yaran kasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma.

Mai magana da yawun rundunar, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewaya ya ce sun sheke ƴan bindigar da dama amma ba a san inda Turji yake ba.

Ya ce sojojin sama sun far wa ƴan ta'addan tare da haɗin guiwar sojojin ƙasa, suka kashe wasu daga cikinsu yayin da wasu kuma suka arce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.