Rikicin Masarautar Kano: Aminu Ado Bayero Zai Daukaka Kara zuwa Kotun Koli

Rikicin Masarautar Kano: Aminu Ado Bayero Zai Daukaka Kara zuwa Kotun Koli

  • Aminu Babba Danagundi bai gamsu da hukuncin da alkalin kotun daukaka kara ya yanke a shari’ar sarautar Kano ba
  • ‘Dan majalisar nadin Sarkin zai tafi kotun koli domin ganin an yi watsi da maido Muhammadu Sanusi II da aka yi
  • Ko shekara nawa za ayi ana zarya a kotu, basaraken ba zai karaya ba domin ganin nasarar Mai martaba Aminu Ado Bayero

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Aminu Babba Danagundi wanda yana tare da Mai martaba Aminu Ado Bayero ya fito ya fadi matsayarsu bayan hukuncin babban kotu.

Kotun daukaka kara ta zartar da hukuncin da bai yi wa Alhaji Aminu Ado Bayero dadi ba, ta na mai tabbatar da aikin gwamnatin jihar Kano.

Sarkin Kano
Rikicin Sarkin Kano za ta je kotun koli Hoto: @kanoemirate01/@MSII_dynasty
Asali: Twitter

A yammacin Lahadi, Daily Trust ta rahoto Aminu Babba Danagund ya na cewa za su kalubalanci hukuncin alkalin kotun daukaka karar.

Kara karanta wannan

Lauya ya fadi hanyar da ta ragewa Aminu Ado bayan nasarar Sanusi II a kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminu Babba Danagundi shi ne ya je kotu ya na mai ja da dawo da Muhammadu Sanusi II da gwamnatin NNPP tayi a matsayin Sarkin Kano a 2024.

Lauyoyin Aminu Ado za su koma kotun koli

Basaraken yake cewa tun ranar Juma’a ya umarci tawagar lauyoyinsa su nemi takardun hukuncin shari’ar domin ganin sun daukaka kara.

Danagundi ya ce kamar yadda aka sani, idan ba a gamsu da hukuncin kotun daukaka kara ba, za a iya tafiya kotun Allah ya isa da ke birnin Abuja.

Aminu Ado bai gamsu da hukuncin kotu ba

Tun da aka fito daga kotun, Danagundi ya ce ya sanar da duniya rashin gamsuwarsa da yadda alkalin babban kotun ya dubi karar da suka kai.

Gabriel Kolawole ya fake da shari’ar Sarkin Muri, a nan kotun koli ta zartar da cewa babu ruwan kotun tarayya da rigimar sarauta a jihohi.

Kara karanta wannan

'Muna kan tsari': Abba Kabir ya magantu bayan hukuncin kotu, ta ba yan Kano shawara

Wanda ya shigar da karar ya ce sauran alkalan sun sabawa Mai shari’a Gabriel Kolawole don haka ya dage sai an kuma gwabzawa a kotun koli.

Akasin yadda wasu suke tunani, Danagundi ya ce ba wai kotu ba ta yarda da bukatar lauyoyinsu ba ne, sai dai kotun ba ta da hurumi ne.

Alhaji Babba Danagundi yake cewa an maida karar zuwa alkalin alkalan jihar Kano da nufin a sake yin shari’ar a wata kotu ta dabam.

Wasa farin girki a rikicin masarautar Kano

Ganin yadda aka yi shekara da shekaru ana shari’ar Mustafa Jikolo da gwamnati, Danagundi yana ganin yanzu aka fara shari’a da gwamnati.

A maganarsa, ya ce babu wanda ya isa ya fara farin ciki domin ba a gama shari’a ba tukuna, The Guardian ta kawo wannan labari da yamman nan.

Yaushe Aminu Ado zai bar fadar Nassarawa?

Game da gidan Nassarawa da Aminu Ado Bayero yake ciki, basaraken ya ce kotu ta yi hukunci cewa a bar shi ya zauna tare da ba shi tsaro.

Kara karanta wannan

'Ta koma kanku': Abin da Sanusi II ya ce bayan hukuncin kotu kan rigimar sarauta

Sannan ya tunawa al’umma cewa kafin yanzu ya shafe shekaru 17 ya na shari’a da Marigayi Ado Bayero, bai ki a yi ta fama a kotu ba.

Lauya ya ce Aminu Ado ya rasa sarauta

Ana da labari Muhammed Bello Buhari ya ce Muhammadu Sanusi II ya yi galaba a kotu kuma lauyan bai ganin Aminu Ado Bayero zai dawo.

MB Buhari ya kira hukuncin da aka zartar da nasara ga gwamnatin da ta dawo da shi gadon sarauta, ya ce sai dai kuma a tari zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng