Laifuffukan yanar gizo: Tinubu da gwamnoni 36 sun shiga matsala, an jero zarge zarge kansu
- Kungiyar SERAP ta kai Bola Tinubu da gwamnoni 36 kotu kan amfani da dokar laifuffukan yanar gizo (Cybercrimes) don tauye 'yancin fadin albarkacin baki
- Kotun ECOWAS ta yanke hukunci cewa sashi na 24 na dokar Cybercrimes a 2015 ya saba wa hakkin dan Adam, amma ba a aiwatar da sauye-sauye ba
- SERAP na zargin cewa dokar tana da ma'ana mai wahalar fahimta da kuma barazana ga masu fafutuka, 'yan jarida da masu amfani da kafofin sadarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar tabbatar da adalci da shugabanci na gari, SERAP ta shigar da kara kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da gwamnoni 36.
Kungiyar ta shigar da korafi ne kan amfani da dokar laifuffukan yanar gizo (Cybercrimes) wajen tauye 'yancin fadin albarkacin baki da hakkin dan Adam.
SERAP ta maka Tinubu, gwamnoni a kotu
Kungiyar ta tabbatar da haka ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a yau Lahadi 12 ga watan Janairun 2025 a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar SERAP ta ce ana tauye hakkin dan Adam musamman ga masu fafutuka da 'yan jarida, masu rubutun ra'ayi, da masu amfani da kafofin sada zumunta.
Duk da cewa dokar Cybercrime (Amendment) Act 2024 ta soke sashi na 24, ta kasa magance matsalolin kunci da rashin fahimta da dokar ke da su.
A karar da aka shigar a kotun ECOWAS mai lamba ECW/CCJ/APP/03/2025, SERAP tana kalubalantar doka ta Cybercrime ta 2024, tana mai cewa ba ta da daidaito da 'yancin fadin albarkacin baki.
“Sabon dokar Cybercrimes ta 2024 ya bude kofa ga hukunta fadin albarkacin baki cikin gaskiya, yana takura masu fafutuka, 'yan jarida, masu rubutun ra'ayi, da masu amfani da kafofin sada zumunta.”
“Abin da ake nufi da ‘haddasa karya doka da oda’ a cikin sashi na 24(1)(b) yana da rudani, wanda zai iya haifar da zalunci ga masu fadin gaskiya.”
“Maimakon amfani da dokar wajen kare yanar gizo da masu amfani da ita, mahukuntan Najeriya suna amfani da ita wajen tauye hakkin dan Adam da 'yancin 'yan jarida.”
- Cewar SERAP
Fargabar da SERAP kan dokar laifuffukan yanar gizo
Kungiyar ta ce sashe na 24 na Cybercrimes na 2024, da kuma sashi na 58 wanda ya bayyana wasu abubuwa da ke barazana ga 'yancin dan Adam.
“Sabuwar dokar ba ta samar da cikakkun matakan karewa daga amfani da ita wajen zaluntar masu bin gaskiya ko fadin albarkacin baki.”
- SERAP
Tsare yara: SERAP ta ba Tinubu wa'adi
Kun ji cewa Ƙungiyar SERAP ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta umartar a saki yaran da aka tsare saboda zanga-zanga.
Ƙungiyar ta ce tsare yaran ya tauye musu haƙƙin da suke da shi na zuwa neman karatu a makaranta da sauran hakkokinsu.
Wannan na zuwa ne bayan zargin yaran da aka tsare da hannu a zanga-zangar da aka gudanar kan halin kunci da aka shiga.
Asali: Legit.ng