N40bn Ta Yi Kadan: INEC Ta Fadawa Majalisa Biliyoyin da Take So a Ware Mata a 2025
- Hukumar INEC ta yi watsi da kasafin kuɗi na Naira biliyan 40, tana neman Naira biliyan 126 don gudanar da ayyukan zaɓe a 2025
- INEC ta shaidawa majalisar tarayya cewa akwai bukatar a kara yawan kudin kasafinta saboda tsadar gudanar da zaɓubbuka
- Kwamitin majalisar ya nuna goyon baya ga INEC, yana mai tabbatar da cewa za a ɗauki matakan magance matsalolin hukumar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi watsi da Naira biliyan 40 da aka ware mata a kasafin kuɗi na 2025.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya nemi Naira biliyan 126 don gudanar da ayyukan hukumar cikin nasara a shekarar 2025.
Wannan batu ya bayyana yayin zaman kare kasafin kuɗin hukumar INEC a gaban kwamitin haɗin gwiwa na majalisar tarayya, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
N126bn: INEC ta nemi karin kasafin 2025
A ranar Juma’a, Farfesa Yakubu ya bayyana muhimmancin karin kuɗin, yana mai jaddada cewa gudanar da zaɓe a Najeriya na da tsadar gaske.
Farfesa Yakubu ya ce:,
“Domin cimma nasarori a ayyukanmu, muna bukatar sama da Naira biliyan 126 a kasafin kudin 2025 da aka gabatar.
“Mun shirya takardun da ke ɗauke da bayanin yadda za mu kashe Naira biliyan 126, kuma yin yi bayanin a mataki-mataki.”
INEC ta ce albashin ma'aikata zai lashe N40bn
Farfesa Yakubu ya ce Naira biliyan 40 da aka ware ba za ta rufe ko kashi ɗaya bisa uku na kuɗin da hukumar za ta kashe ba.
Ya bayyana cewa kudin ma’aikata kadai, musamman saboda sabon mafi ƙarancin albashi, zai cinye duk abin da aka ware a kasafin kuɗin.
A 2024, hukumar ta dogara ne kan tallafi don gudanar da zaɓen gwamnan Edo da Ondo, wanda ya ci Naira biliyan 10.5 da doriya.,
INEC ta goyi bayan karawa INEC kudi
INEC ta bayyana cewa nauyin gudanar da zaɓe a Najeriya yana da girma sosai, tana mai jaddada muhimmancin samun isasshen kuɗi.
Farfesa Yakubu ya nemi majalisar dokoki da ta shirya wani taron tattaunawa tsakanin INEC da ‘yan majalisa don magance matsalolin zaɓe a Najeriya.
‘Yan kwamitin sun nuna goyon bayansu kan neman ƙarin kuɗin, inda suka tabbatar da cewa za su yi aiki don tabbatar da samun isasshen kuɗi ga hukumar.
Shugaban kwamitin zaɓe na majalisar wakilai, Balogun Adebayo, ya ce dole ne a tabbatar da cewa INEC ta kasance mai cikakken ikon gashin kanta.
"INEC ta kashe N355bn kan BVAS" - Dele Momodu
A wani labarin, mun ruwaito cewa iƙirarin Dele Momodu, ɗan takarar fidda gwani na PDP, cewa INEC ta kashe N355bn kan BVAS, ba gaskiya ba ne.
Binciken kasafin kuɗin zaɓe na 2023 ya nuna INEC ta kashe N117.1bn kan fasahar zaɓe, ciki har da na’urar BVAS wanda ke nufin kudin BVAS bai kai N335bn ba.
Asali: Legit.ng