An Shiga Tashin Hankali a Kebbi da 'Yan Ta'addan Lakurawa Suka Kashe Ma'aikata 4
- Wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan ta’addan Lakurawa ne sun kai hari Kebbi, inda suka kashe ma’aikatan kamfanin Airtel uku
- Wani ma’aikacin asibitin Sir Yahaya ya shaida cewa uku daga cikin wadanda aka kawo asibitin ma’aikatan shige da fice ne
- Kwamishinan ‘yan sanda ya tura jami’an tsaro zuwa wurin da aka kai harin, bayan ya nemi hadin kan mutanen kauyen Gumki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kebbi - 'Yan ta’addan kungiyar Lakurawa sun kashe ma’aikatan wani babban kamfanin sadarwa guda uku a Kebbi.
Wannan harin na zuwa ne kasa da awanni 48 bayan da 'yan ta'addan suka kashe wasu jami'an 'yan sanda guda biyu.
Lakurawa sun kashe mutane a Kebbi
Maharan sun kai farmaki ne a wani wurin da ake gine-gine a kauyen Gumki da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma’aikatan da suka mutu suna girka hasumiyar tsaro ta Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya lokacin da aka kai musu hari.
Bayan kashe mutum uku da wani wanda ba a gano sunansa ba, mayakan Lakurawa sun yi awon gaba da wasu kayan aiki a wurin.
Duk da cewa rahoton ‘yan sanda ya ce ma’aikatan Airtel ne aka kashe, mazauna yankin sun ce na Hukumar Shige da Fice ne.
An tura dakaru domin kwaso gawarwakin mutanen
Wani ma’aikacin asibitin Sir Yahaya ya ce mutum uku daga cikin wadanda aka kawo sun kasance ma’aikatan Hukumar Shige da Fice.
Kakakin ‘yan sanda na jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da mutuwar mutum hudu, daya mazaunin yankin, uku kuma ma’aikatan Airtel.
Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, CP Bello M. Sani, tare da kwanturola na hukumar shige da fice, sun tura jami’ai zuwa wurin domin daukar gawarwakin.
'Yan sanda sun nemi hadin kan mazauna Kebbi
CP Bello ya kara tura wasu tawagogin dabarun tsaro zuwa yankin domin dakile hare-haren ‘yan ta’adda da ke ci gaba da addabar al’umma.
Kwamishinan ya gana da mazauna yankin, inda ya roke su da su rika ba da hadin kai ga jami’an tsaro don samun gaggawar daukar mataki.
Ya kuma bayyana cewa al’ummar yankin na taka muhimmiyar rawa wajen samar da bayanai da ke taimaka wa ‘yan sanda wajen yaki da ta’addanci.
An ba sojoji umarnin kawo karshen Lakurawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojojin Najeriya ta umarci dakarun Operation Fansan Yamma da su kawar da ƴan ƙungiyar ta'addanci ta Lakurawa.
Wannan umarni ya fito ne daga kwamandan rundunar haɗin gwiwa da ke kula da Arewa maso Yamma, Oluyinka Soleye, a ranar Juma’a.
Kwamandan ya bayar da wannan umarni ne yayin ziyararsa ga dakarun sojojin da ke Balle, hedikwatar karamar hukumar Gudu a Sokoto.
Soleye ya yi kira ga sojojin da su kasance masu sadaukarwa ga aikin su, yana mai tabbatar musu da cikakken goyon bayan hedkwatar rundunar.
Asali: Legit.ng