Ana Raɗe Raɗin Zai Koma APC, Gwamna Ya Kori Kwamishina daga Aiki
- Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya kori kwamishinan yaɗa labarai, Dokta Ifeanyi Osuoza daga aiki nan take
- Wannan mataki dai na zuwa ne a daidai loƙacin da ake yaɗa jita-jitar gwamnan na shisshigewa jam'iyyar APC kuma da alamun zai iya barin PDP
- An ruwaito cewa Gwamna Sheriff Oborevwori ya umarci kwamishinan ayyuka ya kula da ma'aikatar yaɗa labarai kafin ya naɗa wanda zai maye gurbin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya sauke kwamishinan yaɗa labarai, Dokta Ifeanyi Osuoza, daga mukaminsa.
Wannan mataki ya kasance wani muhimmin sauyi a gwamnatin jihar, wanda ke nuna aniyar gwamnan wajen sake fasalin gwamnati don inganta ayyukanta.
Meyasa Gwamna Oborevwori ya kori kwamishinan?
Jaridar The Nation ta tattaro cewa babu wani cikakken bayani kan dalilin da ya sa Gwamna Oborevwori ya kori kwamishinan daga aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai tuni Dokta Osuoza ya samu takardar sanarwa daga gwamnatin jihar Delta game da wannan mataki na kora da gwamnan ya ɗauka.
Darakta janar na hukumar na hukumar wayar da kan jama'a da yaɗa labarai na jihar Delta, Dr. Fred Latimor Oghenesivbe ya ce:
"An sanar da tsohon kwamishinan yaɗa labarai, Ifeanyi Osuoza halin da ake ciki."
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa korar kwamishinan na da alaƙa da rahotannin rashin gamsuwa da aikinsa daga wasu bangarorin gwamnati da al’ummar jihar Delta.
Haka nan kuma matakin ya zo daidai da lokacin da ake yaɗa jita-jitar Gwamna Oborevwori na shirye-shiryen barin PDP zuwa APC.
Gwamnan Delta ya naɗa kwamishinan riko
Bisa ga rahotanni, Gwamna Oborevwori ya umarci Charles Aniagwu, wanda shi ne kwamishinan ayyuka (hanyoyin karkara), da ya kula da ma’aikatar yaɗa labarai na ɗan lokaci.
Ana sa ran Aniagwu zai fara wannan aiki a matsayin na rikon kwarya daga ranar Litinin mai zuwa, har sai an sanar da sabon kwamishinan yaɗa labarai.
Charles Aniagwu ba bako bane a fannin yaɗa labarai, ya yi aiki a matsayin sakataren yaɗa labarai (CPS) da kwamishinan yaɗa labarai a lokacin mulkin tsohon Gwamna Ifeanyi Okowa.
Hakan ya ba shi ƙwarewa da gogewa a aikin sadarwa da yaɗa manufofin gwamnati ga jama’a.
Mutanen Delta sun fara ce-ce-ku-ce
Sauyin da aka yi ya haifar da ce-ce-ku-ce daga jama'a, inda wasu ke ganin hakan na nuna karfin gwiwar gwamna wajen kawar da duk wani abin da zai iya rage wa gwamnatin jihar tasiri.
Wasu kuma na ganin wannan wani mataki ne da za a iya amfani da shi don dawo da kwarjinin ma’aikatar, musamman idan aka yi la’akari da mahimmancin yada labarai a ci gaban jihar.
Gwamnan Delta ya musanta shirin komawa APC
Kun ji cewa Gwamna Sheriff Oborevwori ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya fara shirin ssuya sheƙa daga PDP zuwa APC.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Delta, Sir Festus Ahon ya fitar a ranar Litinin da ta gabata, ya ce wannan jita-jitar ba ta da tushe balle makama.
Asali: Legit.ng