'Ta Koma Kanku': Abin da Sanusi Ii Ya Ce bayan Hukuncin Kotu kan Rigimar Sarauta

'Ta Koma Kanku': Abin da Sanusi Ii Ya Ce bayan Hukuncin Kotu kan Rigimar Sarauta

  • Yayin da kotu ta yi hukunci kan rigimar sarauta a Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi wa Allah godiya
  • Sarki Sanusi II ya bukaci al'ummar jihar Kano su cigaba da addu'ar zaman lafiya da kuma neman tsari daga nasu ta da fitina
  • Basaraken ya yi addu'a Ubangiji ya jawo wa masu neman fitina a Kano fitintinu a rayuwarsu da kuma tashin hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana bayan hukuncin kotu kan rigimar masarauta a jihar a jiya Juma'a 10 ga watan Janairun 2025.

Basaraken ya yi godiya ga Ubangiji kan hukuncin kotu game da rigimar sarauta inda ya ce wannan babbar nasara ce gare su.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya magantu bayan hukuncin kotu kan rigimar sarauta
Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi wa Allah godiya bayan hukuncin kotu kan rigimar masarauta. Hoto @masarautarkano.
Asali: Twitter

Sanusi II ya yi addu'a kan masu jawo fitina

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun tarfa ƴan bindiga, sun hallaka sama da 100

Sarkin ya yi addu'ar Allah ya kona duk wani mai shirin rura wutar fitina a Kano a cikin wani faifan bidiyo da @RakaFatima ta wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce wannan fada da mulkin Allah ake yi kuma shi bai bukatar taimakon kowa a kowane irin yanayi.

"Assalamu alaikum warahmatullah wa barka tuhu, muna amfani da wannan rana ta Jumaa mu kaddamar da nasiha ga jama'a da fatan wadanda suka ji za su isar ga wadanda ba su ji ba."
"Babban maudu'i shi ne kara kira ga jama'a a ci gaba da tafiyar da lamura cikin kwanciyar hankali da biyayya da doka da oda."
"Kamar yadda aka sani a yau masarauta ta samu babbar nasara a kotu inda Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da cewa babban kotu ba ta da hurumi ta saka baki a harkar masarauta."

- Muhammadu Sanusi II

Sanusi II ya caccaki masu korafi a kotu

Kara karanta wannan

Hadimin Gwamna Abba ya fadi abin da zai faru da Aminu Ado Bayero a karshe

Basaraken ya kuma soki alkalin kotun da kuma wadanda suka saka alkalin yanke hukunci da cewa sun sani ba su da hurumin yin hakan.

"Wannan hukunci dama sananne ne, wadanda suka je kotun sun san ba ta da hurumi, shi alkalin da ya ba da umarni ya san ba shi da hurumi."
"Waɗanda suka saka alkalin ya ba da umarni sun sani ba shi da hurumi amma an yi haka saboda ana neman kawo son zuciya da rigima a wanna kasa."
"Babbar nasiharmu ita ce har yau Allah ya kare rayukan mutanen jihar Kano kuma ya tsare su daga tashin hankali, muna kira ga mutane a kiyaye wannan zaman lafiya."

- Cewar Sarki Muhammadu Sanusi II

Sarki Sanusi II ya bukaci al'umma da su ci gaba da addu'a domin samun zaman lafiya a Kano da kuma yin adalci tsakanin al'umma.

Hukuncin kotu: Hadimin Abba Kabir ya magantu

Kara karanta wannan

Wani shugaban karamar hukuma ya sake nada hadimai 130 watanni 6 da nadin mutum 100

A wani labarin, kun ji cewa Hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Hassan Sani Tukur ya zargi wasu shugabanni a APC suke amfani da Aminu Ado Bayero a rikicin masarautar Kano.

Mai ba gwamnan shawara ya na zargin jam’iyyar APC mai adawa za su sanya basaraken nadama ne idan aka gama shari’ar da ake yi game da sarautar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.