Gwamnan Arewa Mai Sukar Kudirin Harajin Tinubu Ya Sauya Ra'ayi, Ya Fadi Dalili

Gwamnan Arewa Mai Sukar Kudirin Harajin Tinubu Ya Sauya Ra'ayi, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnan jihar Nasarawa wanda na ɗaya daga cikin masu sukar ƙuɗirin harajin gwamnatin mai girma Bola Ahmed Tinubu, ya sauya ra'ayi
  • Abdullahi Sule ya bayyana cewa ya suya ra'ayinsa ne kan sukar ƙudiron saboda an magamce damuwar da yake da ita a kansa
  • Gwamnan ya nuna cewa tun da farko baya son a amince da ƙudirin harajin ne a asalin tsarin da aka fito da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana dalilin da ya sa ya sauya ra’ayinsa kan ƙudirin gyaran haraji na gwamnatin Bola Tinubu.

Gwamna Sule ya bayyana cewa ya sauya ra'ayi ne nan ƙudirin da ya haifar da cece-kuce, saboda an magance damuwar da yake da ita a kansa.

Gwamna Sule ya sauys ra'ayi kan kudirin haraji
Gwamna Sule ya ce an yi gyara kan kudirin haraji Hoto: Abdullahi Sule, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Gwamna Sule, wanda ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin Arewa masu nuna adawa da ƙudirin tun farko, ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Politics Today na tashar Channels TV.

Kara karanta wannan

"Za a haura N70,000": Gwamnatin Tinubu za ta ƙara mafi ƙarancin albashi a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamna Sule ya sauya ra'ayi?

Ya bayyana cewa adawarsa ba ta kasance da ra’ayin gyaran haraji ba, amma tana da nasaba da abubuwan da ke cikin ƙudirin.

A cewarsa, burin da aka sa a gaba shi ne a tabbatar da cewa an tattauna kan ƙudirin sosai kafin a yanke wani hukunci.

"Mun cimma burinmu, kuma wannan ne dalilin da ya sa a yau nake magana daban. Ina magana daban saboda burin da muke son cimmawa ya riga ya tabbata."
“Mun so a tattauna ƙudirin sosai kuma ka da amince da shi a asalin tsarin da aka fito da shi. Yanzu, akwai damar sake dubawa, kuma ina yabawa majalisar wakilai, musamman shugaban majalisar, saboda yadda suka tafiyar da batun."

- Abdullahi Sule

Ya yabawa kan ƙudirin harajin Bola Tinubu

Gwamnan ya nuna gamsuwarsa da yadda ƴan majalisa, musamman na majalisar wakilai da shugaban ta, suke tafiyar da ƙudirin a yanzu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Gwamna Abba ya fadi abin da yake ci masa tuwo a kwarya kan tazarce

Ya ce damuwar da ya nuna tare da wasu mutane ta sa an sake nazarin ƙudirin sosai.

Gwamna Sule ya kuma bayyana cewa irin wannan tattaunawa tana da muhimmanci, wajen tabbatar da cewa duk wani ƙudiri da zai shafi jama’a an aiwatar da shi cikin adalci da kuma la’akari da buƙatun jama’a.

Wannan canjin matsayi ya nuna cewa ana iya samun fahimta ta tsakani idan aka ba dukkanin ɓangarori dama su tattauna da kuma bayyana ra’ayinsu kan duk wani al’amari da ya shafi jama’a.

Ƙudirin harajin dai ya sha suka sosai musamman daga Arewacin Najeriya inda ake tunanin cewa zai yi wa yankin illa.

Gwamna Sule ya yi garambawul a gwamnati

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi zazzaga a gwamnatinsa bayan ya yi wani ƙwarya-ƙwaryar garambawul.

Gwamna Abdullahi Sule ya kori sakataren gwamnatin jihar (SSG) daga muƙaminsa tare da rusa majalisar zartaswar jihar gaba ɗayanta.

Gwamnan wanda bai bayyana dalilin ɗaukar matakin ba, ya kuma kori dukkanin hadimansa da kwamishinonin da ke cikin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng