Dakarun Sojojin Najeriya Sun Tarfa Yan Bindiga, Sun Hallaka Sama da 100

Dakarun Sojojin Najeriya Sun Tarfa Yan Bindiga, Sun Hallaka Sama da 100

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 120 tare da cafke wasu miyagu 105 da ake zargi a mako guda
  • Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba ya ce sojojin sun ceto mutane 43 da aka yi garkuwa da su a sassan kasar nan
  • Ya ce sojojin sun kwato miyagun makamai daga hannun ƴan ta'addan a samamen da suka kai tsakanin 4 zuwa 10 ga watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hedikwatar Tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa dakarun soji sun sami nasarori da dama a yaƙi da 'yan ta'adda da masu tayar da kayar baya a mako guda.

Dakarun sojojin sun kashe 'yan ta'adda 120, sun kama wasu 105, tare da ceto mutane 43 da aka yi garkuwa da su a hare-haren da suka kai tsakanin ranar 4 zuwa 10 ga Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya halarci taron MNJTF a ƙasar waje, ya ba iyalan sojoji tallafin N300m

Dakarun sojojin Najeriya.
Hedkwatar tsaro ta bayyana nasarorin da sojoji suka samu a mako guda a Najeriya Hoto: DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Wannan na daga cikin jerin nasarorin da sojojin ke samu a fafutukar da suke yi don tabbatar da zaman lafiya a sassan Najeriya, in ji rahoton Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun sami galaba kan ƴan ta'adda

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kan ayyukan sojoji a makon jiya.

Ya ce dakarun rundunar Operation Haɗin Kai, wadda ke aiki a yankin Arewa maso Gabas, ta yi nasarar kashe 'yan ta'adda 64 ta hanyar hare-haren sama.

Haka kuma, sojojin sun kama wasu mutane 28 da ake zargi da hannu a ayyukan ta'addanci.

A Arewa maso Yamma a cewar kakakin DHQ, dakarun Operation Fansan Yamma sun kai farmaki kan wasu sansanonin 'yan ta'adda, inda suka kashe 21 daga cikinsu.

Ya ƙara da cewa sun kama mutane 24 da ake zargi, tare da ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Ndume ya yi goma ta arziki ga mutanen Borno da harin Boko Haram ya shafa

Kakakin DHQ ya ƙara da cewa A Arewa ta Tsakiya kuwa, dakarun Operation Safe Haven sun kama miyagu 14 tare da ceto mutane 11.

Dakarun sojoji sun ƙwato makamai

Bugu da ƙari, sojojin sun kwato makamai daban-daban, ciki har da bindigogi 3 da aka ƙera a gida, harsasai 23.

"A wani aikin daban da aka gudanar a wannan yanki ta hannun rundunar Operation Whirl Stroke, an kama mutane 5 masu tsattsauran ra’ayi da ake zargi, tare da ceto mutane 3," in ji Buba.

Wannan nasarorin sun jaddada irin ƙoƙarin da dakarun Najeriya ke yi wajen tabbatar da tsaron ƙasa da tsaron al’umma.

Manjo Janar Buba ya yi kira ga jama'a su ba da haɗin kai don ganin an kawo ƙarshen matsalolin tsaro a Najeriya.

Sojoji sun muƙushe babban ɗan bindiga

A wani labarin, kun ji cewa sojoji sun kashe wani hatsabibin ɗan bindiga da ya damu al'umma a jihar Katsina, Alhaji Ma’oli.

Mutane da dama a jihar da ke Arewa maso Yamma sun yaba da wannan nasara da sojoji suka samu, sun ce za a samu sauƙi bayan kashe ɗan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262